Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da ginin babban asibitin Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda

A ranar Talatar nan ne Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da ginin babban asibitin Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, wanda aka yi masa gyara, tare da wadata shi da kayan aiki.

Babban asibitin, yana kula da Ƙauran Namoda da maƙwabtan ta, wanda kuma aka wadata shi da kayan aiki don ya samar da ingantacciyar kiwon lafiya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar yau a Gusau, ya bayyana cewa babban asibitin, an samar masa da kayan aikin kula da lafiya, waɗanda suka haɗa da na’urorin binciken cututtuka, gadajen haihuwa, na’urar auna bugun zuciya (ECG), na’urorin binciken jini, babbar na’urar binciken jini ta ‘automatic hematology analyzer’, na’urar auna nauyi ta zamani, fitilar haskawa yayin aikin tiyata da dai wasu kayan kula da lafiya da daman gaske.

Sanarwar ta ƙara da cewa, asibitocin gaba ɗaya na da matuƙar muhimmanci wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya, wanda ya kamata ya zama mai sauƙi ga al’ummar Jihar Zamfara.

A wajen ƙaddamar da aikin, Gwamna Lawal ya nanata cewa babban abin da gwamnatinsa ta mayar da hankali a kai shi ne farfaɗo da taɓarɓarewar ababen more rayuwa da magance matsalolin da ke addabar dukkanin sassan tattalin arzikin jihar.

“Wannan hangen nesa ya sa muka yanke shawarar samar da ajandar kawo sauyi da ta ƙunshi ginshiƙai shida, inda kiwon lafiya ya kasance ginshiƙi na uku, biyo bayan ilimi da tsaro.

“Manufarmu na farfaɗo da asibitoci shi ne mu tabbatar da cewa an samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga jama’ar mu, walau a yankunan karkara ko a birane. Wannan fahimtar ta sa muka gyara tare inganta cibiyoyin kiwon lafiya da suka lalace, musamman a garuruwa masu muhimmanci irin su Kaura Namoda, da ke a tsakanin ƙananan hukumomi da kuma zama wuri mafi sauƙi ga yankunan da ke kewaye.

“Na yi farin cikin bayar da rahoton cewa, a cikin watanni 14 da suka gabata, mun samu gagarumin ci gaba wajen inganta fannin kiwon lafiya ta hanyar zuba jari wajen gyara da inganta asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a faɗin jihar nan.

“Har ila yau, mun kammala shirye-shiryen ɗaukar ma’aikatan kiwon lafiya da horar da su, sayen magunguna da kayan aiki masu muhimmanci, da gabatar da ayyukan kula da lafiyar mata da yara kyauta.

“Muna fatan waɗannan ayyukan za su haifar da ingantacciyar lafiya ga jama’armu ta hanyar rage mace-macen mata masu juna biyu, mace-macen jarirai, da daƙile cututtuka a faɗin jihar.

“Bikin ƙaddamarwar na yau ya nuna aniyarmu ta samar da ingantaccen kiwon lafiya ga ɗaukacin mazauna Zamfara, ba tare da la’akari da wurinsu, matsayinsu ko kuɗin da suke samu ba.

“Tsarin aikin ya haɗa da sake gyara asibitin gaba ɗaya, tare da samar da tsayayyen wutar lantarki mai ƙarfin 32 kW, da sanya fitulun titi 25, da kuma samar da muhimman kayan aiki ga likitoci. Bayan kammala wannan ginin cikin nasara, ina da yaƙinin cewa mutanen Kaura Namoda da garuruwa da ƙauyukan da ke maƙwabtaka da su, yanzu za su samu damar cin moriyar kiwon lafiya mai sauƙi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *