Gwamna Dauda Lawal ya amince, tare da sanya hannu a dokar taƙaita zirga-zirgar babura a jihar Zamfara.
A Alhamis ɗin nan ne gwamnan ya rattaba hannun a fadar gwamnatin jihar da ke Gusau.
A cikin wata sanarwa da Kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa Majalisar tsaro ta jihar ne ta yanke shawarar taƙaita zirga-zirgar baburan, a wani taron gaggawa da suka gudanar ranar Laraba.
Sulaiman Bala ya ce, don ganin an aiwatar da wannan doka, Antoni Janar na jihar, Abdul’aziz Sani SAN ne ya gabatar wa da gwamnan dokar mai lamba No. 07, 2024, inda kuma ya amince da ita.
“A yau, Gwamna Dauda Lawal ya rattaba hannu a dokar taƙaitawa, tare da haramta zirga-zirgar babura daga ƙarfe 8 na dare zuwa ƙarfe 6 na safe a duk faɗin jihar Zamfara.
“An yi wannan doka ne a ƙoƙarin da ake yi na kare rayuka da dukiyar jama’a, a kuma rage ayyukan ta’addanci da ya addabi jama’a, da kuma ƙarfafa wa ƙoƙarin gwamnati na maganin rashin tsaro a jihar.
“Saboda haka, daga yanzu an haramta zirga-zirgar babura gaba ɗaya daga ƙarfe 8 na dare zuwa ƙarfe 6 na safe a duk faɗin jihar.
“Babu wani babur da aka amincewa ya hau titi a jihar nan a tsakanin waɗannan awoyi da aka ambata. An ba jami’an tsaro izinin kama duk wanda ya karya wannan doka.
“An baiwa Antoni Janar na jihar Zamfara damar ya hukunta duk wanda aka kama ya keta wannan doka.”