Gwamna Dauda Lawal ya yi alƙawarin kulawa da iyalan jami’an Askarawan Zamfara da aka kashe

Gwamna Dauda Lawal ya yi alƙawarin cewa gwamnatin sa za ta bayar da cikakkiyar kulawa ga iyalan jami’an Askarawan Zamfara da aka kashe a wani kwanton ɓaunar da aka yi masu.

Gwamnan ya yi wannan alƙawarin ne a fadar ‘Yan Doton Tsafe lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan jami’an Askarawan Zamfara da ‘yan bindiga suka yi wa kwanton ɓauna a cikin makon da ya gabata.

Yayin jajanta wa masarautar da kuma Iyalan waɗanda aka kashen, Gwamna Lawal ya nuna cewa wannan sadaukarwa da jami’an suka yi, ba za ta tafi a banza ba.

A cikin wata sanarwa da ya fitar yau a Gusau, Mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya ambato Gwamna Lawal yana cewa: “Na zo nan yau ne domin in miƙa ta’aziyyata ga masarauta, iyalai da al’ummar Tsafe bisa kisan da aka yi wa gwarazan mu, a wani kwanton ɓauna da aka yi masu.

“Wannan wani bala’i ne wanda muka ji raɗaɗin sa matuƙa. Lallai mun shaida wannan tsayin-daka na waɗannan dakaru don kare rayukan al’ummar su.

“Ina jin wannan baƙin labari, sai na turo da wata ƙaƙƙarfar tawaga ta gwamnati, ƙarshin jagorancin Mataimakin Gwamna domin su zo su miƙa ta’aziyya ga masarauta da iyalan waɗanda abin ya shafa.

“Ina tabbatar maku da cewa irin waɗannan abubuwan, ba za su dakatar da mu daga farmakin mu ke kai wa ‘yan bindiga ba. Muna yin duk abin da ya wajaba wajen kawo ƙarshen ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

“Gwamnatin jihar Zamfara za ta ɗauki duk ɗawainiyar iyalan waɗannan Asakarawan. Ina yin wannan alƙawari ne a nan, kuma za mu tabbatar mun cika shi.

Nan take kuma Gwamnan ya bayyana bayar da tallafin kuɗaɗe da kayan abinci ga iyalan mamatan.

A jawabin da ya gabatar, Sarkin Tsafe, Alhaji Muhammadu Bawa, ya nuna godiyar sa ga Gwamna Lawal, da kuma jijina masa bisa irin namijin ƙoƙarin da ya ke yi wajen samar da tsaro da jin daɗin al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *