Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Binciken Bidiyon Da Ake Yi Wa Dan-Balki Kwamanda Bulala

Daga Wakilanmu

An ja hankalin gwamnatin jihar Kaduna game da wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, inda aka nuna wasu da ba a san ko suwanene ba su na yi wa Dan Balki Kwamanda bulala bisa zargin shi da zagin Gwamna Uba Sani.

Gwamnatin jihar Kaduna dai ta nisanta kan ta daga mummunan lamarin, ta na mai cewa hakan ba ya da hurumi a duk wata al’umma tagari, don haka ta na nan a kan bakan ta na mutunta tsarin bin doka da oda.

Haka kuma, gwamnatin jihar Kaduna ta ce tsarin shugabancin ta an gina shi ne a kan adalici da daidaito da kuma mutunta dan Adam.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai na gwamnatin jihar Kaduna Muhammad Lawal Shehu, ta ce tun bayan hawan ta mulki a cikin watan Mayu na shekara ta 2023, gwamnatin jihar kaduna a karkashin jagorancin Satana Uba Sani, ta ke aiki babu kama hannun yaro domin farfado da yarda atsakanin al’umma, ta yadda za a tafi da kowane dan asalin jihar.

Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin jihar Kaduna ta na maraba da shawarwarin al’umma, sannann ta bude kofar da kowa zai iya bayyana ra’ayin sa a siyasance.

Ta ce Gwamnan jihar Kaduna ya kwashe tsawon lokaci ya na fafutukar kare ‘yancin dan Adam, don haka har yanzu ya na kan bakan shi na tabbatar da ganin ba a tauye hakkin kowane bil-Adama ba bisa tsarin doka da oda.

Tuni dai Gwamna Uba Sani ya bada umurnin a gudanar da kwakkwaran bincike a kan mumman lamarin, sannan ya lashi takobin bin diddigin yadda lamarin ya faru, tare da bada tabbacin cewa duk mai hannu a aika-aikar dole ya fuskanci hukuncin abin da ya aikata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *