Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya karɓi baƙuncin sabuwar babbar Sakatariya a gwamnatin tarayya

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya karɓi baƙuncin sabuwar babbar Sakatariya a gwamnatin tarayya mai wakiltar jihar Zamfara.

A Juma’ar nan ne aka bayyana sunan Dr. Maryam Ismaila Keshinro, tare da wasu mutum bakwai a matsayin sabbin manyan sakatarori a ma’aikatun gwamnatin tarayya.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar yau a Gusau, ya bayyana cewa a Lahadin nan ne Gwamna Lawal ya karɓi baƙuncin Dr. Maryam don nuna mata goyon baya da ƙarfafa gwiwa.

Bayan da ya taya Dr Maryam Murna, Gwamna Dauda Lawal ya hore ta da ta kasance Jakadiyar jihar Zamfara tagari.

“Ina so in yi amfani da wannan dama wajen taya ki murnar kasacewa babbar Sakatariya a gwamnatin tarayya.

“Wannan wata dama ce da mu ke sa rai, tare da yi maki addu’ar amfani da ita wajen yi wa ƙasar nan bauta, tare da bayar da gudumawa wajen sake gina wannan jiha ta mu.

“Gwamnatin jihar Zamfara za ta samar maki da duk irin gudumawar da za ta taimaka maki wajen ci gaba, muna alfahari da nasarorin da kika samu a rayuwa.

“Na karɓi baƙuncin ki a yau ne don in nuna maki ƙauna, sannan in sanar da ke cewa muna alfahari da ke a jihar Zamfara.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *