Gwamnan Zamfara ya jaddada dawo da martabar kasuwanci a jihar

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya ƙara jaddada aniyar sa ta sake gina Zamfara don dawo da matsayin ta na dandalin kasuwanci a Arewacin Nijeriya.

Gwamnan ya bayar da wannan tabbacin ne a lokacin gudanar da bikin ƙaddamar da fara ginin tashar tashi da saukan jiragen sama, wanda Ministan harkokin Sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya ƙaddamar jiya a Gusau.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu jiya, ta bayyana cewa filin jiragen saman da ke Gusau da za a gina, zai zama wani ingantaccen wuri ne da za a rinƙa hidimar harkar jiragen ƙasar nan da na ƙasashen waje.

Kakakin Gwamnan ya ƙara haske da cewa, wannan aiki zai haɗa da gina layin tashin jirage mai kilomita 3.4 don jirage masu zirga-zirga, sanya fitilu a layin, da sauran na’urorin da ke taimaka wa tashi da sauran jirage.

Wani ɓangare na jawabin Gwamna Lawal, ya ƙara jaddada cewa gwamnatin sa ta duƙufa wajen tabbatar da jihar Zamfara ta shiga fagen gogayya a harkokin kasuwanci, wanda zai jawo hankalin masu zuba jari daga ciki da wajen ƙasar nan.

Ya ce, “Mai girma Minista, manyan baƙi, maza da mata, ‘yan jarida, wannan tashar jirgin saman za ta ƙunshi wurin tashin jirage irin na zamani da yanayi mai kyau ga fasinjoji, wanda zai haɗa da wurin tantancewa, wurin duba jakunkuna irin na zamani, wuraren jira, da kuma wuraren jami’an Kwastam da na shige da fice. Bugu da ƙari, tashar nan za ta samu ingantaccen sashen kula da hada-hadar jirage, wanda zai ƙunshi na’urorin sadarwa irin na zamani.

“Haka kuma, wurin zai ƙunshi gina sashen kula da gyare-gyare, sashen kashe gobara da ceto, wurin ajiyar man jirgi, hanyoyin zuwa tashar jirgin, wuraren ajiye ababen hawa ga fasinjoji da ma’aikata, samar da isasshe kuma ingantaccen ruwa, isasshiyar wutar lantarki da na’urorin sadarwa.

“Wannan tashar jirgin sama ta Gusau, tsararre ne da zai ƙunshi duk wani fanni na tashi da saukar jirage daga sassan ƙasar nan da na ƙasashen waje, zai zama wata mahaɗa ta yankin. Kowane irin jirgi zai iya sauka a wurin, zai samar da sassauƙar hanyar shiga da fita jihar Zamfara, tare da inganta mu’amala, kasuwanci da yawon buɗe ido.

“Kamfanin gine-gine na ‘Triacta Nigeria Limited’ ne zai gudanar da aikin, bisa shawarar kamfanin ‘JBI Tech Consult’, bisa yarjejeniyar kammala aikin a tsakanin watanni 30.

“Akwai amfani mai yawa da ke ƙunshe a harkar gina wannan tashar jirgi ta Gusau, musamman a fannin tattalin arziki, domin zai samar da hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da kuma inganta zamantakewa da alaƙa da jihar Zamfara. Zai samar da hanyar shiga jihar mu kai tsaye ta jiragen sama, wanda zai kawar da wahalhalun da ‘yan kasuwa ke sha wajen jigilar hajojin su.”

Tun farko a nasa jawabin, Ministan sufurin jiragen sama na ƙasar nan, Festus Keyamo ya bayyana cewa Zamfara ta kasance koma-baya a harkokin ci gaba, a daidai lokacin da sauran jihohin yankin Arewa maso Yamma su ke da ingantattun filayen jiragen sama, amma ita ba ta da shi, duk da kasancewar ta cibiyar noma a yankin.

Ministan ya ce, “Amma dai ba a makara ba. Wani ɗan jarida daga ƙasar waje ya kira ni yana tambaya ta ko Zamfara na buƙatar tashar jirgin sama. Ina da yaƙinin cewa samar da tashar jiragen sama a Zamfara, ba wai ga haɓaɓaka karkar kasuwanci kawai ya tsaya ba, zai inganta harkar walwala da jin daɗin jama’a. Bisa abubuwan da na lura da su, lallai jihar a shirye ta ke wajen wannan ci gaba.

“Ina so in dawo nan a shekara mai zuwa don ƙaddamar da jigilar maniyyata aikin Hajji. Maniyyatan jihar Zamfara sun kwashe shekaru dama suna shan wahala wajen hawa jirgi zuwa ƙasa mai tsarki. Wannan ba zai sake faruwa ba. Don haka ina tabbatar wa da ɗan uwana, Gwamna Dauda Lawal cewa, ina bayan ka, ina tare da kai, ina tare da al’ummar jihar Zamfara don ganin wannan mafarki ya zama gaskiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *