Gwamnan Zamfara Ya Kai Ziyarar Ta’aziyya Garin Mada

  • Ya sha alwashin hukunta waɗanda suka kashe Malamin

A yau Juma’a ne Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya ziyarci garin Mada domin yin ta’aziyyar rasuwar babban Limamin garin, Marigayi Sheikh Abubakar Mada.

Idan za a iya tunawa, wasu da ake zargin ’yan banga ne suka kashe Sheikh Abubakar Hassan Mada a makon jiya a garin Mada da ke Ƙaramar Hukumar Gusau ta Jihar Zamfara.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa Gwamna Lawal ya yi sallar Juma’a ne a masallacin garin Mada.

A cewar sanarwar, Gwamnan ya miƙa ta’aziyya ga iyalan marigayi Sheikh Abubakar Hassan Mada, Hakimin gundumar, da sauran al’ummar yankin.

A yayin jawabinsa ga jama’a bayan sallar Juma’a, Gwamna Lawal ya yi alƙqwarin yin duk mai yiwuwa don ganin an yi adalci a kan lamarin.

“Na zo nan ne domin in tabbatar wa mutanen garin Mada cewa gwamnatina ta himmatu wajen ganin an tabbatar da adalci, tare da hukunta waɗanda suka aikata wannan aika-aika.

“Babu wani abu da za a bari wajen ganin an tabbatar da adalci a kan kisan Sheikh Abubakar. Za mu yi aiki tuƙuru don ganin cewa marigayi Sheikh da iyalansa sun samu adalcin da ya kamata,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta nakalto gwamnan yana cewa, “Bana Gusau lokacin da lamarin ya faru, amma bayan na samu wannan labari mai tada hankali, nan take na tuntuɓi shugabannin hukumomin tsaro da abin ya shafa a jihar domin ɗaukar matakin da ya dace”.

“’Yan sanda sun fara gudanar da bincike cikin gaggawa kan kisan gillar. Na rantse da Allah za mu tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi a wannan ɗanyen aikin, za a hukunta shi,” in ji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *