Gwamnati za ta gina babbar tashar mota ta zamani a Gusau

A taron majalisar zartarwar jihar, wanda ya gudana Talatar nan a fadar gwamnatin jihar da ke Gusau, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da gina babbar tashar mota irin ta zamani a garin Gusau a wani ɓangare na aikin sabunta birane a Jihar.

A ranar Talatar nan ne gwamnan ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa na musamman da shugabannin Jihar Zamfara a gidan gwamnati da ke Gusau.

Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, a cikin watar sanarwar da ya fitar yau a Gusau, ya bayyana cewa majalisar ta tattauna muhimman batutuwa da za su amfanar da Jihar Zamfara.

A cewarsa, majalisar ta amince da bayar da kwangilar gina tashar mota ta zamani ga kamfanin Fieldmark Construction Ltd, wanda adadin kuɗinsa ya kai Naira 4,854,135,954.53.

Aikin gina wannan tashar, wani muhimmin ɓangare ne na shirin sabunta birane a jihar, kuma zai inganta hanyoyin sufuri da sauƙaƙa rayuwa a jihar.

Ma’aikatar Kula da Ƙananan Hukumomi da Ma’aikatar Kasuwanci, Masana’antu da Yawon Buɗe Ido ne za su ɗauki nauyin aikin tare, yayin da Ma’aikatar Ayyuka da Samar da Ababen More Rayuwa za ta sa ido a kan yadda za a gudanar da aikin.

Tuni Ma’aikatar Ayyuka ta tsara tare da samar da wani ƙudiri na cikin gida don gudanar da aikin tare da miƙa shi ga Ofishin Kula da Harkokin Ƙasa da Ƙasa na jihar, wanda bai kushe komai ba game da wannan ƙudiri.

Babbar tashar ajiye motoci ta zamanin ta ƙunshi abubuwa da dama kamar; gina ofisoshin gwamnati da ƙungiyoyi, kafa ofishin kashe gobara, gina masaukin baƙi, samar da asibiti, kafa ofishin ‘yan sanda, ƙirƙirar ɗakin ajiye kaya, samar wurin POS, da kafa garejin gyaran mota da wurin wankin mota.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *