Daga Abubakar Musa
Gwamnatin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma matsayar musayar fursunoni da Hamas a awowin farko na safiyar ranar Asabar, wanda hakan ke nuni da cire wani shamaki domin samar da sauki ga zirin Gaza da yaki ya yiwa illa.
Kamar yadda kafar watsa labaru ta The New Arab ta ruwaito, ministoci sun kada kuri’a inda 24 suka amince 8 suka nuna rashin amincewa a kan matsayar tsagaita wutar bayan awanni shida na tattaunawa a Jerusalem, inda hakan ya samar da hanya ga faruwar tsagaita wutar da ake jiran kasancewarta a safiyar ranar Lahadi.
Karamar majalisar tsaron Isra’ila tun da farko ta nemi ministocin da su amince da tsagaita wutar, inda zai haifar da tsagaita wuta a tsakanin bangarorin biyu na makonni shida, wanda hakan zai sa motocin agaji su shiga zirin da ke a zagaye.
A karkashin shiga tsakanin da Katar, Misra da Amurka suka yi, Isra’ila za ta saki ‘yan kurkuku Falasdinawa sama da 1700 a yayin da Hamas za ta saki akalla 33 cikin 94 da ta yi garkuwa da su da ke cigaba da kasancewa a Gaza.
Isra’ila za ta fara janyewa daga wasu bangarorin zirin yayin da motocin agaji 600 za a bari su rinka shiga a kullum inda hakan zai samar da kayayyakin bukata na abinci da magani ga al’ummun wadanda ke karkashin kawanyar da Isra’ila ta yi masu na tsawon watanni.
Isra’ila dai ta lalata mafi yawan zirin tare da kashe Falasdinawa kusan 47,000 tun bayan da Hamas ta kaddamar da harin 7 ga watan Oktobar 2023, kodayake bincike na baya-bayan nan ya nuna cewa kididdigar wadda ta ke a hukumance na iya kasancewa wadda ta yi kasa sosai da hakikanin alkaluman.