Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi watsi da zargin da aka yi mata na cewa ta ware Naira Biliyan 19.3 don sayen kayan kicin a shekarar 2024, inda ta bayyana cewa ana yaɗa waɗannan ƙarairayi ne don a kautar da hankalin jama’a.
A ranar Talata ne wata kafar sadarwa ta wallafa cewa kasafin kuɗin jihar Zamfara ya ware Naira Biliyan 19.3 wajen sayen kayan kicin da na wurin cin abinci a cikin kasafin kuɗin shekarar 2024.
Cikin martanin da ya mayar kan wannan zargi, a wani taron manema labarai da ya gabatar a Gusau, Kwamishinan kasafi da tsare-tsare, Mallam Abdulmalik Gajam ya nuna takaicin sa game da wannan ƙagaggen rahoto.
Mallam Gajam bai tsaya nan ba, sai da ya fayyace dalla-dalla yadda gaskiyar abin ke game da waɗannan kuɗaɗe Naira Biliyan 19.3, da aka ware ma wasu ayyuka a mai’aikatar ilimi. “Wannan kafar sadarwa da ta yaɗa wannan labari, sai ta tsakuro wani ɓangare na kasafin, ta kau da kai ga muhimman fannonin da cikakken kasafin ya ƙunsa.”
Gajam ya ci gaba da cewa, “Tsarin yadda aka kasafta Naira Biliyan 19.3 a ƙarƙashin ma’aikatar ilimi yana nan a layin manyan ayyuka.
“Sunan da ke ciki na Wurin Cin Binci da Kicin, yana ƙunshe ne cikin rukunin wasu ayyuka, waɗanda suka haɗa da shirin nan na AGILE, gina makarantun Firamare na yanki, samar da makarantar Firamare ta musamman a Gusau, sawo kayan aikin kicin da na dafa abinci ga duk makarantun gwamnati a kan Naira Miliyan 40, gina cibiyar horar da Malamai, da ƙirƙiro da shirin asusun ci gaban Malamai.
“Duk waɗannan ne suka haɗu suka tara Naira Biliyan 19.3.
Kwamishinan ya kuma yi ƙarin haske da cewa, gwamnatin Gwamna Dauda Lawal ta zo ne domin ta rage ɓarnatar da dukiyar Baitulmali, tare da rufe duk wasu hanyoyin sata. “Ba za a taɓa samun mu cikin irin wannan rashin iya aiki da aikin banza ba.”