Gwamnatin Tarayya ta jaddada ƙudirin ta na zurfafa alaƙar ta da ƙasar Indonesiya, tare da mai da hankali kan batun tattalin arziki da kuma hanyoyin haɗin gwiwa.
An tabbatar da hakan ne a taron Indonesiya da nahiyar Afrika karo na biyu, wanda ake gudanarwa daga ranakun 1 zuwa 3 na Satumba, 2024, a Bali, babban birnin ƙasar.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, wanda ya wakilci Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, shi ne ya jagoranci tawagar Nijeriya zuwa Babban Taron Haɗin Gwiwa na Masu Ruwa da Tsaki da kuma Taron Shugabanni a ƙasar da ke nahiyar Asiya.
Ministan ya nanata ƙudirin Nijeriya na ƙulla ƙawance da Indonesiya, yana mai cewa dukkan yankunan biyu suna da abubuwa da yawa da za su samu daga ƙara haɗin gwiwa a fannin kasuwanci, zuba jari, da musayar ilmi da ƙwarewa.
Ya ce: “Taron Indonesiya da Afirka wata hanya ce ta haɗin gwiwa, da nufin ciyar da ƙasashen mu biyu zuwa makoma mai haske da wadata.”
Idris ya ƙara da cewa, “Nijeriya ta ƙudiri aniyar yin amfani da ƙarfin da muke da shi da albarkatun mu don mai da hankali kan muhimman ginshiƙai kamar sauyin tattalin arziki, makamashi da haƙar ma’adinai, samar da abinci da lafiya, da tattalin arziki na dijital.
“Waɗannan su ne ginshiƙan da za a gina haɗin gwiwar mu a nan gaba, tare da zurfafa haɗin gwiwa da cigaban tattalin arziki mai ɗorewa wanda zai amfani dukkan al’ummomin mu.”
Taron ya jaddada gagarumin ƙarfin tattalin arziki da al’ummar Afirka da Indonesiya suke da su, waɗanda ke wakiltar sama da mutane biliyan 1.7 da jimillar ƙarfin tattalin arziki na GDP na dalar Amurka tiriliyan 4.4.
Taron ya tattaro shugabannin ƙasashe, jami’an gwamnati, ‘yan kasuwa, da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban, inda suka tattauna haɗin gwiwar tattalin arziki, da magance matsalolin duniya, da kuma lalubo hanyoyin samun cigaba mai ɗorewa tare.
Jagorancin Nijeriya wajen ciyar da ajandar Tarayyar Afirka ta 2063 shi ma ya kasance jigon tattaunawa a taron.
Ministan ya yi bayani kan cikakkiyar ajandar Shugaban Ƙasa Tinubu ta sauye-sauyen tattalin arziki, tsaro, shugabanci, da cigaban al’umma a matakin ƙasa, da kuma ƙoƙarin da yake yi na inganta harkokin kasuwanci a yankin, da ababen more rayuwa, da kwanciyar hankali a siyasance ta hanyar jagorancin sa a Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).
An bayyana rawar da Nijeriya ke takawa a Yankin Kasuwanci na Nahiyar Afirka (AfCFTA) a matsayin babbar hanyar bunƙasa kasuwanci da masana’antu a cikin Afirka.
Taron, wanda ya samu halartar wakilai daga ƙasashen Afirka 22 da kuma wasu ƙasashe biyar da ba na Afirka ba, ya kuma tuna da taron nahiyoyin Asiya da Afirka na shekarar 1955, wanda aka fi sani da “Bandung Spirit”, wanda ya aza harsashin dangantakar Asiya da Afirka.
Taron ya yi kira da a ƙara inganta yin mu’amala a tsakanin nahiyoyi ta fuskar kasuwanci, zuba jari, da haɗin gwiwar raya ƙasa.
An jaddada cewa kamata ya yi Afirka ta zarce matakin mai fitar da ɗanyen man fetur kawai, ta zama cibiyar samar da kayayyaki, tare da ba da tabbaci na musamman ga ayyukan bututun iskar gas da ke ratsa sahara tsakanin Nijeriya da Aljeriya da kuma Morokko.
Taron na Indonesiya da Afirka ya kasance wani dandali na ƙarfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin Indonesiya da ƙasashen Afirka.