GWAMNATIN TARAYYA TA SAKI NAIRA BILIYAN 50 DOMIN KYAUTATA WALWALAR MA’AIKATAN JAMI’O’I – MINISTAN ILIMI

Ministan Ilimi na Najeriya, Dakta Maruf Olatunji Alausa, ya sanar da sakin kudade har Naira biliyan 50 da gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta amince da su domin biyan hakkokin ma’aikatan jami’o’in tarayya.

Wannan mataki yana daga cikin cikar alkawurran shugaban kasa Tinubu wajen inganta harkar ilimi da tabbatar da zaman lafiya a cibiyoyin ilimi.

Ministan ya bayyana cewa, “Wannan ba kawai biyan kudi ba ne, alama ce ta yadda shugaban kasa ke mutunta rawar da malamai da ma’aikatan jami’o’i ke takawa wajen gina makomar matasan Najeriya.”

Ya kara da bayyana godiyar gwamnatin tarayya ga kungiyoyin malamai da ma’aikata bisa hadin kai da fahimtar juna da suka nuna, wanda hakan ya kawo dadadden zaman lafiya a jami’o’in kasar.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa, “Matasa su ne zuciyar kasar nan. Goben su na da matuƙar amfani gareni da gwamnati na. Tabbatar da matasan mu sun sami karatu abu ne mai muhimmaci. Na kuduri aniyar kawo karshen yajin aiki a jami’o’in ƙasar nan gaba daya.”

Wannan mataki na cikin shirin “Renewed Hope Agenda” da ke nuna yadda gwamnatin ke daukar harkar ilimi da muhimmanci domin ciyar da Najeriya gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *