Gwamnatin Tarayya za ta fito da manhajar DSO na aikin talbijin kwanan nan – Minista

 Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris (Na farko daga dama)

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa ma’aikatar sa ta na nan ta na aiki tuƙuru domin fito da sabuwar manhajar da za a yi amfani da ita a koma aiki da na’urar kwamfuta wajen aikin talbijin a duk faɗin ƙasar nan, wato ‘Digital Switch Over’ (DSO).
Hadimin musamman kan harkar yaɗa labarai na ministan, Malam Rabi’u Ibrahim, ya bayyana a cikin wata takardar sanarwa cewa ministan ya faɗi haka ne a Abuja a ranar Litinin a lokacin da ya ke buɗe babban taron sanin makamar aiki na shugabannin gudanarwa na Hukumar Talbijin ta Ƙasa (NTA).
Ya ce: “Ina kuma so in yi amfani da wannan damar in nanata sadaukarwar Gwamnatin Tarayya ga tsarin ‘Digital Switch Over’, domin kuwa Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai ta na ta aiki tuƙuru kan manhajar DSO wadda ba za ta gaza ba; wadda za a yi amfani da ita a birane da ƙauyukan Nijeriya. Ana sa ran cewa hukumar NTA, a matsayin ta na babbar mai ruwa da tsaki a tsarin na DSO, za ta taka muhimmiyar rawa a ciki.”
Don haka Idris ya ƙalubalanci NTA da ta yi zuzzurfan tunani kan yadda yanayin aikin jarida ya ke sauyawa, musamman da yake sababbin fasahohin zamani na shigowa kuma zaɓin masu kallo shi ma ya na canzawa tare da kawo ƙalubale da kuma damarmaki.
Ya ce: “Sadaukarwar mu ga tabbatar da inganci da kuma karɓar sauyi shi ne gaba da komai. Tilas ne NTA ta ci gaba da rungumar canji, ta na karɓar sababbin dabaru a yayin da ta ke riƙe da darajar aikin jarida mafi girma sau da ƙafa.
“Wannan taron ya zo ne a daidai lokacin da masu kallo su ke ta samun zaɓi daban-daban na inda za su samu bayanai, musamman ma da yake yanzu soshiyal midiya na da ƙarfi tare da tasiri wajen yaɗa labaran ƙarya da yaudara da ke akwai a cikin ta; don haka muhimmancin taro irin wannan ba ƙarami ba ne.” 
Ya lura da cewa ɗaga ƙarfin hotuna da sautin da aka samu a NTA daga matakin ‘standard definition’ (SD) zuwa matakin ‘high definition’ (HD) ya na yin tasiri matuƙa a wajen jama’a masu kallo, ya ƙara da cewa tilas ne a samar da wannan tsarin a dukkan tashoshin NTA da ke faɗin ƙasar nan idan ana so a cimma manufar da ake buƙata. 
 
Dangane da batun Tsarin Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda) na gwamnatin Shugaba Tinubu kuwa, wanda ya bayyana da cewa ba a taɓa samun dabarar gina ƙasa ta ɓangaren zamantakewa da tattalin arziki a Nijeriya kamar ta ba, don haka a cewar Idris, “haƙƙi ya rataya a wuyan NTA ta ci gaba da wayar da kan ‘yan Nijeriya kan nasarorin da ake samu a dukkan ɓangarori, kuma ta tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya sun fahimci alƙiblar da gwamnatin Tinubu ta fuskanta wajen yaɗa labarai da tsara shirye-shiryen talbijin. 
Ministan ya buƙaci NTA da ta dage wajen dawo da martabar da aka san ta da ita a da lokacin da abubuwan da ta ke kai wa masu kallo, musamman wasannin kwaikwayo, waɗanda ban da haɓaka harkar nishaɗi a talbijin da su ka yi a ƙasar nan har ma sun kasance dalilin da ke sa mutane na rugawa gida domin yin kallo da yamma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *