Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce babban abin da gwamnatin Tinubu ta fi mayar da hankali a kai ba shi ne ta ɗora wa ‘yan Nijeriya wahala ba, sai dai ta gyara munanan tsare-tsare da matakan da ba su dace ba waɗanda a tarihi suka kawo cikas ga cigaban Nijeriya.
A wata sanarwa da Mataimakin Ministan na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Rabi’u Ibrahim, ya fitar, Idris ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Laraba yayin da yake ganawa da jami’an diflomasiyya a Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙasar dangane da zanga-zangar da aka yi a faɗin ƙasar.
Ya jaddada ƙudirin Shugaba Tinubu na aiwatar da gyare-gyare da nufin samar da cigaba mai ɗorewa da kuma inganta rayuwa ga ɗaukacin ‘yan ƙasa, yana mai cewa ƙalubalen da ake fuskanta a yanzu na wucin-gadi ne.
Ministan ya ce, “Yana da muhimmanci mu fara da wannan bayanin: cewa Shugaba Tinubu bai zo ofis don ya jawo wahalhalu ko kuma wahalar da ’yan Nijeriya ba. Ya zo ne don warware matsalolin baya; tare da yunƙurin gyara da yawa daga cikin tsare-tsaren da ba su da kyau da kuma matakan da ba su dace ba da suka kawo mana koma-baya a matsayin mu na ƙasa shekaru da yawa.”
Ya ƙara da cewa, “Shugaban Ƙasa ya hau karagar mulki ne a ɗaya daga cikin lokuta mafi ƙalubale a tarihin Nijeriya, inda ƙasar ke kashe kashi 97 na dukkan kuɗaɗen shigar ta wajen biyan basussuka; tare da yawaitar talauci, hauhawar rashin aikin yi, lalacewar ababen more rayuwa, da rashin tsaro. Yayin da take fuskantar waɗannan abubuwa masu ban tsoro, gwamnati ta ɗauki ƙwararan matakai tare da aiwatar da gyare-gyaren da aka daɗe ba a yi ba domin ceto tattalin arziƙin ƙasar daga durƙushewa.”
Ministan ya bayyana cewa kawar da tallafin man fetur ya zama dole don karkatar da kuɗaɗen zuwa sassa masu muhimmanci kamar kiwon lafiya, ilimi, ababen more rayuwa, da tsaro, wanda ke tasiri kai tsaye ga jin daɗin ’yan ƙasa da ci gaban ƙasa.
Ya amince da cewa ana shan raɗaɗin sauyin da ke tattare da wannan matakin kuma ya yi nuni da cewa Gwamnatin Tarayya ta tsara shirye-shiryen shiga tsakani don magance waɗannan ƙalubale.
“Mun dage sosai kan tabbatar da cewa an aiwatar da waɗannan ayyukan domin kawo sassauci ga ‘yan Nijeriya,” inji Idris.
Yayin da yake magana kan zanga-zangar da aka gudanar a faɗin ƙasar nan, ministan ya ce gwamnati na mutunta ‘yancin yin taro cikin lumana da ‘yancin faɗin albarkacin baki, waɗanda su ne ginshiƙin dukkan al’ummomin dimokiraɗiyya, amma ya jaddada cewa abin da ya fara a matsayin zanga-zangar lumana a wasu jihohi da kuma Babban Birnin Tarayya shi ne ba da jimawa ba wasu da suka kutsa kai cikin zanga-zangar suka karɓe ragamar tare da shirya tarzomar da ta lalata rayuka da dukiyoyi.
“An samu rahotannin ƙone-ƙone, ɓarna, sace-sace, da kuma arangama da jami’an tsaro a garuruwa da dama. Abin takaici, waɗannan al’amura sun yi sanadin asarar rayukan da ba su ji ba ba su gani ba da kuma asarar dukiya mai yawa,” inji shi.
Idris ya tabbatar wa da jami’an diflomasiyya cewa Gwamnatin Tarayya ta fara gudanar da bincike kan tashe-tashen hankulan da aka yi a lokacin zanga-zangar domin a gano tare da gurfanar da duk masu hannu a cikin lamarin.
Ya ce: “Mun himmatu wajen hana sake aukuwar irin wannan mummunan lamari a nan gaba.”