Gwamnatin Zamfara, ta ƙaddamar da rabon tireloli 135 na takin zamani

A wani gagarumin yunƙuri na bunƙasa ayyukan noma, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da rabon tireloli 135 na takin zamani ga manoma a faɗin ƙananan hukumomin jihar 14.

An ƙaddamar da rabon takin ne a ranar Talata a Ma’aikatar Noma ta jihar Zamfara, inda aka ajiye takin.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta ce, za a raba buhunan taki iri-iri 81,000 kyauta ga manoma 40,500 a faɗin ƙananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara.

Sanarwar ta ƙara da cewa, a wajen ƙaddamar da shirin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada aniyar gwamnatinsa na haɓaka noma a Zamfara ta hanyar taimakawa manoma wajen bunƙasa noman su. “Za mu ci gaba da ƙoƙarinmu don magance ƙalubale a fannin noma.”

Gwamnan ya ce, “Mun ƙuduri aniyar tunkarar ƙalubale da kuma bai wa manoman mu goyon baya da ƙarfafa musu gwiwa don tabbatar da ci gaban al’umma da tattalin arzikin jihar.

“A ’yan watannin da suka gabata na ziyarci ɗaukacin ƙananan hukumomi 14 domin ƙaddamar da rabon takin zamani da sauran kayayyakin noma ga manoman mu a ƙarƙashin shirin NG-CARES. Taki wani muhimmin abu ne na samar da amfanin gona yayin da yake haɓaka samar da abinci, yana ƙara yawan amfanin gona, da haɓaka ingancin kayan amfanin gona.

“Za mu ci gaba da yin aiki tuƙuru domin tabbatar da cewa noman bai taƙaita da damina kaɗai ba, ya zama abu ne da ake yi a duk faɗin shekarar wanda manoman mu za su kasance cikin aiki a koda yaushe. Ta yin haka, za mu iya cimma burinmu na samun ikon mallakar abinci da kuma ƙara samun kuɗin shiga na manoma.

“Kafin in kammala, ina kira ga waɗanda suka amfana da wannan karimcin da su yi amfani da waɗannan takin yadda ya kamata. Ina kuma ƙara tabbatar muku da irin goyon bayan da muke bayarwa wajen samar da yanayi mai kyau ga noman noma a faɗin jihar nan domin bai wa manoman mu damar komawa gonakinsu ba tare da wata fargaba ba.

“Da waɗannan kalamai, abin alfaharina ne na ƙaddamar da rabon tireloli 135 na taki iri-iri ga manoma a faɗin ƙananan hukumomin jiharmu 14 domin noman damina a jihar Zamfara a shekarar 2024.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *