Gwamnatin Zamfara Ta Fara Biyan Kuɗaɗen Barin Aiki Da Tsofaffin Ma’aikata Ke Bi

A halin da  ake ciki, gwamnatin jihar Zamfara ta fara biyan kuɗaɗen barin aiki (Gratuety) ga ma’aikatan da suka bar aiki a duk faɗin jihar, wanda ya kai ma Naira Biliyan 13.4.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta bayyana cewa an cimma wannan matsaya ce sakamakon wani kwamiti da gwamnatin ta kafa don tantance sahihancin tsofaffin ma’aikatan, tun daga shekarar 2011 zuwa yau.

Idris ya ce, a sakamakon haka, yanzu nan tsaffin ma’aikatan da suke bin bashin haƙƙin barin aiki, tun daga shekarar 2011 zuwa yau, sun fara karɓar kuɗaɗen su. 

Yana mai cewa duk wasu basussukan barin aiki na shekara da shekaru, yanzu an tantance su, kuma tun a ranar Alhamis da ta gabata aka fara biya. 

Sanarwar ta Idris ta kuma bayyana cewa, “Gwamnatin jihar ta ɗauki ƙwararan matakai don magance basussukan da tsofaffin ma’aikata ke bi, waɗanda suka haɗa da haƙƙin waɗanda suka rasu, waɗanda suka bar aiki da masu aikin wucin-gadi.

“Gwamna Dauda Lawal ya kafa wani kwamiti da zai tantance bayanin tsohon ma’aikaci, tare da sahihahcin sa don biyan bashin da ake bi, tun daga shekarar 20221.

“Bayan wannan tantancewa ce, sai gwamnatin ta gano cewa tsofaffin ma’aikatan gwamnatin jijar, da na Ƙananan Hukumomi na bin bashin Naira Biliyan goma sha Uku da Miliyan Huɗu N13.4b). 

“Yanzu haka an fara biyan duk waɗanda aka tantance, tun ranar Alhamis. Gwamnatin za ta tabbatar da an tantance duk wani tsohon ma’aiktaci, kuma an biya shi haƙƙin sa, ba tare da wahalarwa ba.”

A ƙarshe, sanarwar ta bayyana cewa, “Gwamnan jihar Zamfara na cika alƙawarin da ta yi na jagorancin da zai ceto al’umma, tare da sake ɗaukaka jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *