Farfesa Yakubu ya na karɓar hatimin karramawa daga hannun Madam Davidetta Browne Lansanah a birnin Monrovia
Hukumar Zaɓe ta Laberiya (NEC) ta yi jinjina da damƙa kambin yabo ga Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, bisa ƙoƙari da muhimmiyar rawar da ya taka wajen ƙara wa dimokiraɗiyya karsashi a ƙasar.
Wannan karramawa ta fito ne daga Shugabar Hukumar Zaɓen Laberiya ɗin, Madam Davidetta Browne Lansanah, a ranar Juma’a, a Monrovia, babban birnin ƙasar.
An damƙa masa kambin girmamawar ne a wurin taron sanin makamar aiki da aka shirya wa ma’aikatan hukumar zaɓen Laberiya, wanda Yakubu ne ya gajoranci horaswar.
A cikin jawabin ta, Lansanah ta nuna farin ciki da gamsuwa da irin basira da kyawawan tsare-tsaren da INEC da Yakubu su ka shimfiɗa wa Hukumar Zaɓen Liberiya, wanda ta ce ya ƙara wa matakan shirya zaɓuɓɓukan ƙasar inganci da nagarta.
Ta nuna godiya ga Farfesa Yakubu, a madadin Hukumar Zaɓen Laberiya, bisa ga gagarumar rawar da ya taka wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da matakan kafa dimokuraɗiyyar a Laberiya.
Da ta ke tuna rawar da gudunmawar da ya bayar a matsayin sa na Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Hukumomin Zaɓe na Ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), Lansanah ta lissafo yadda ya tafiyar da ƙungiyar bisa nuna kishin aiki da bin ƙa’idoji. Ta kuma jinjina masa dangane da yadda ya riƙa ba ta goyon baya a matsayin ta na Shugabar Hukumar Zaɓe ta Laberiya.
Da ya ke nuna godiya bisa karimcin da aka yi masa, Farfesa Yakubu ya bayyana farin ciki dangane da karramawar da Hukumar Zaɓen Laberiya ɗin ta yi wa INEC.
Haka kuma ya nuna muhimmancin nagartattun ayyuka da tsare-tsaren da ma’aikatan INEC su ka bijiro wa ma’aikatan hukumar zaɓen Laberiya.
Ya tuno da irin rawar da INEC ta bayar lokacin tsare-tsaren shirya zaɓen shugaban ƙasa a Laberiya da aka yi cikin 2017, sai kuma gudunmawar da INEC ɗin ta bayar a zaɓen raba-gardama cikin 2020, wanda ECOWAS ta gudanar.
Yakubu ya nuna yadda INEC ta taimaka wa hukumar zaɓen Laberiya wajen gina wa ƙasar turbar rajistar masu zaɓe ta hanyar tsarin na’urar tantance masu katin rajista.
Farfesa Yakubu da sauran mahalartan taron