Bafalasdinen da ya fi kowanne dadewa a kurkukun Haramtacciyar Kasar Isra’ila, Nael Barghouti, wanda ya yi sama da shekaru 40 a kurkuku, ya shaki iskar ‘yanci a ranar Alhamis karkashin musayar ‘yan kurkuku da wadanda aka yi garkuwa da su karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Kamar yadda kungiyar fafutika ta ‘yan kurkuku Falasdinawa ta shaida, Barghouti ya yi shekaru 45 ne a kurkuku inda ya yi 30 a jere.
Kamar yadda ya ke a rahoton The New Arab, Barghouti ya iso kasar Misra a ranar Alhamis bayan an fitar da shi daga yankin Falasdinu bayan fitowar ta shi.
Barghouti an fara kama shi ne a shekarar 1978 an kuma yanke ma shi hukuncin rai-da-rai a kurkuku saboda hari kan jami’in HKI da kuma wurare mallakar HKI. A wancan lokacin shi mamba ne a Fattah, wadda tafiya ce ta shugaban Falasdinawa a yanzu haka Mahmoud Abbas, wadda ke adawa da Hamas.
An taba sakin Barghouti sau daya a shekarar 2011 a wani bangare na musayar Falasdinawa ‘yan kurkuku da kuma sojan Isra’ila da Hamas ta kama. Sai aka yi masa daurin talala a Kubar, a Gabar Yamma da Kogin Jordan. Sai aka sake kama shi a shekarar 2014, kuma ya bar Fatah ya koma Hamas yayin da ya ke a cikin kurkuku.