Yamanawa Sun Sake Kai Hari Kan Wasu Jiragen Ruwa Guda Biyu Na Isra’ila

Daga Ammar M. Rajab

Dakarun kasar Yemen sun kaddamar da hare-hare kan wasu jiragen ruwa guda biyu da ke kan hanyar zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila da ke tafiya a tekun Bahar Maliya a wani yunkuri na ci gaba da matsin lamba ga Isra’ila da kawayenta domin su kawo karshen wuce gona da iri da suke yi akan Falasdinawa a Gaza.

A cikin wata sanarwa ta dandalin sada zumunta na X a ranar Litinin, Kakakin rundunar sojojin kasar Yemen, Birgediya Janar Yahya Saree ya bayyana Swan Atlantic da kuma MSC Clara a matsayin jiragen ruwa biyu da aka kai wa hari a tekun Bahar Maliya da sanyin safiya.

Sanarwar ta ce Yemen ta yi amfani da jiragen yakin ruwa ne marasa matuka wajen kai wa jiragen ruwan hari, inda ta kara da cewa hare-haren na nuna goyon baya ne ga al’ummar Palasdinu dangane da hare-haren da ake kai wa Gaza.

Wannan harin shi ne na baya baya a ci gaba da yakin Yemen matsin lamba ga gwamnatin Isra’ila da Amurka da sauran kawayenta da Yemen ke yi domin kawo karshen yakin Gaza da Isra’ila ta kashe mutane sama da 19,000 tun farkon watan Oktoba.

Gangamin wani bangare ne na yunkurin yaki da Isra’ila a yankin wanda kuma ya shafi kungiyoyin gwagwarmaya a Iraki da Lebanon.

Kwamandan rundunar soja ta biyar ta Yemen, Manjo Janar Yusuf al-Madani ya fada a ranar Litinin cewa, kasar ta su ta Larabawa a shirye take ta mayar da martani kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa a yankin.

Al-Madani ya ce sojojin Yemen za su kara balbalin bala’in wutar da suke kai hare-hare da su domin mayar da martani ga duk wata barazana daga “kowace hadaka da ke neman shiga tsakaninmu da Falasdinu.”

Ya kuma yi gargadin cewa duk wani yunkuri da zai kara tada zaune tsaye a Gaza zai haifar da karuwar tashe-tashen hankula ne a tekun Bahar Maliya.

One thought on “Yamanawa Sun Sake Kai Hari Kan Wasu Jiragen Ruwa Guda Biyu Na Isra’ila

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *