Fata Ga Marasa Galihu Da Kawo Canji A Rayuwar Jama’a
Daga Abdullahi Musa
A ‘yan makonnin da suka gabata ne Hukumar Zakka da Waƙafi ta jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Sheikh Umar Ahmad Kanoma, ta bullo da wasu sabbin hanyoyi da tsare-tsaren taimaka wa wajen canja rayuwar al’umma da kyautata jin dadin da kuma zamantakewarsu.
Hukumar ta ƙarfafa hanyoyin da aka san ta su na jajircewa wajen yi wa al’umma hidima cikin tausayi da adalci, Hukumar ta samu gagarumin ci gaba a ayyukanta na rage radadin talauci da ƙarfafa wa marasa galihu a lokacin Azumin watan Ramadan da ya gabata.
Bisa kulawar sakataren zartaswa, Habib Balarabe Muhammad, Hukumar ta samu gagarumar nasara wajen tallafa wa mabuƙata da marasa galihu.
Hukumar ta Kai ɗaukin gaggawa ga mata masu fama da matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da haifar masu da fata a zukatansu, ta hanyar shirya masu tarukan fadakarwa da nufin kyautata rayuwarsu.
Baya ga samar wa mata da matasa marasa galihu hanyoyin dogaro da kai, Hukumar ta tallafa masu da mahimman kayayyakin koyon sana’a da haɓaka ƙwarewa a tsakaninsu. Wannan tsarin jin kai yana nuna sadaukarwar Hukumar don jindadin marasa galihu.
A cikin watan Ramadan, Hukumar ta kara kaimi, inda ta tallafa wa mutane sama da 40,000 a fadin jihar Zamfara da kayan abinci da taimakon kuɗi.
Bugu da ƙari, Hukumar ta samar da gaɓoɓin roba kyauta ga mutanen da rasa gaɓoɓinsu sakamako hattsura ko ayyukan ‘yan ta’adda da taimaka wa mata masu matsalar cutar yoyon fitsari (VVF). Hakan ya jaddada himmar Hukumar wajen samun damar kiwon lafiya da nufin inganta rayuwar marasa galihu.
Ta hanyar haɗin gwiwa da ƙungiyoyi jin kai kamar; Bright Futures Serious da Organised Crime Prevention Project (SOC), Hukumar ta samar da tsare-tsare don rigakafi da kuma tsarin tallafi, tabbatar da samari masu aikata laifuka sun sami jagoranci na gari a rayuwarsu da nufin ƙarfafa su don kawar da aikata miyagun laifuka a tsakanin al’umma a jihar.
Bayan Eid al-Fitr, Hukumar ta kasance mai himma, tare da yin alƙawarin shigar ɗaruruwan mutane a cikin shirye-shiryen gina rayuwarsu da dabarun haɓaka fasaha. Wannan tsarin sa ido yana nuna sadaukarwarsu ga ƙarfafawa ta dogon lokaci da nufin samar da mafita mai dorewa ga al’umma.
Nasarorin da Hukumar ke samu sun nuna muhimmancin samar da kyakkyawan tsari daa irin tasirin da yake da shi. Tun daga yunkurin agajin gaggawa zuwa shirye-shiryen karfafawa na dogon lokaci, kowane aiki yana kunshe da ka’idojin hadin gwiwa da jin kai da ke cikin Zakka.
Hukumar ta yi alƙawarin kiyaye ƙa’idodin aiki, haɓaka haɗin gwiwa, da bullo da sabbin hanyoyi don magance talauci da kuma fuskantar ƙalubalen tattalin arziki yadda ya kamata.
Tare da jajircewa wajen yi wa al’umma hidima bisa tsarin addinin Musulunci, Hukumar Zakka da Waƙafi ta jihar Zamfara ta tsaya tsayin daka a matsayin wata fitilar da ke haskaka rayuwar marasa galihu da kuma samar masu da fata a rayuwa.