IPOB ta yi gargadi ga gwamnatin Tinubu, kar Kanu ya mutu a tsare

Kungiyar da ke fafutikar kafa kasar Biyafara (IPOB) ta yi ikirarin cewa gwamnatin Nijeriya na son kashe shugaban ta, Nnamdi Kanu, a sashen tsare mutane na jami’an tsaron farin kaya (DSS), inda ta yi gargadin akwai abinda zai biyo baya in wani abu ya faru ga Kanu.

Kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito, kungiyar ta IPOB ta yi gargadin ne a cikin wani jawabi wanda ta bayar a ranar Juma’a wanda kakakin ta, Emma Powerful, ya sawa hannu, inda ta nuna cewa, “A yayin da rashin adalci ya zama doka, turjuya ta zama aikin yi.”

Kungiyar ta IPOB ta bayyana cewa lafiyar Kanu ta kara tabarbarewa a cikin da ake tsare mutanen, inda ta kara da cewa DSS na yin amfani da maganin gwaji da sauransu ga lafiyarsa da ta ta’azzara.

A yayin da ta zargi gwamnatin Nijeriya da tsara kashe Kanu a fakaice ta hanyar yin amfani da sashen shari’a, ta tunatar cewa Nijeriya ba za ta taba kasancewa yadda ta ke ba in Kanu ya mutu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *