Iran za ta kaddamar da makami mai linzami mai nisan kilomita 2000

Shugaban rundunar kare Juyin-juya halin Musulunci na Iran (IRGC) bangaren sojojin ruwa ya bayyana cewa Iran na gaf da kaddamar da makami mai linzami wanda aka kera a Iran mai nisan kilomita 2000 (mil 1,242), wanda hakan zai kara karfi ga karfin da sojojin ruwan suke da shi wanda tuni ya cigaba.

Kamar yadda Press TV ta ruwaito, shugaban rundunar, Rear Admiral Alireza Tangsiri, ya bayyana cewa sabon makami mai linzamin, wanda ake shirin kaddamarwa a sabuwar shekarar Fasha mai zuwa – wadda za ta fara 20 ga watan Maci – zai yi babban taimako ga tsaron Iran, inda ya yi cikakken bayani a kan karfin da sojin ruwan Iran ke da shi.

“Yanzu muna da makamai wadanda za a iya harbawa daga cikin kasar Iran, inda hakan ya magance bukatar harba su daga bakin teku.” Kamar yadda shugaban ya bayyana yayin da ya ke jawabi a wani shirin talabijin mai suna “Fajr of Hope, Powerful Iran” wanda aka watsa jajibirin bukin cika shekara 46 da nasarar da Juyin-juya halin Musulunci ya yi a shekarar 1979 a kasar.

“Da irin wannan cigaban, za mu iya harbo wuraren da ke Tekun Oman daga arewacin (bangaren) Tekun Fasha.”

Ya tabbatar da cewa rundunar cikin nasara ta harba makami mai linzami daga kudancin bangaren yammacin yankin Tabas na Iran, inda ya ce makami mai linzamin cikin nasara ya harbi inda ake so ya harba wanda ke da nisan kilomita 650 (mil 403) a Tekun Oman da ke kudancin kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *