Jagoran harkar Musulunci, Sheikh Ibraheem Zakzaky, ya dawo gida Nijeriya daga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Kamar yadda yake a cikin wani sako da ofishin Shehin Malamin ya wallafa a kafar sada zumunta ta Facebook,Shaikh Zakzaky ya dawo ne a ranar 21 ga watan Fabrairu, 2024, wato ranar Larabar makon jiya kenan, bayan ya shafe watanni sama da hudu a jamhuriyar Musulunci ta Iran, inda ya je neman lafiya tare da mai dakinsa, Malama Zeenah Ibrahim.
Kamar yadda ofishin ya bayyana, tawagar Jagora Shaikh Zakzaky ta samu kyakkyawar tarba daga dubunnan ‘yan uwa da masoya, inda aka yi taron tarbar a babban dakin motsa jiki da ke filin wasanni na ƙasa da ke Birnin Tarayya Abuja.