Jami’an tsaro sun dakatar da taron Nisfu Sha’aban a Abuja

..Amma an canza wuri

Jami’an tsaro cikin shirin yaki sun dakatar da taron Nisfu Sha’aban da ‘yan’uwa musulmi almajiran Shaikh Zakzaky suka fara gabatarwa a Abuja a ranar Juma’ar nan.

Da misalin karfe 3 na ranar Juma’a 15 ga Sha’aban 1446 (14/2/2025) Harkar Musulunci a Nijeriya karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta fara gudanar da gagarumin bikin Nisfu Sha’aban a muhallin ‘Nigerian Airforce Event Center’ da ke Abuja.

Taron, wanda aka fara shi da addu’a da karatun Alkur’ani, sannan ziyarar Imamul Asr (AJ), Sayyid Abdullahi Ashura ne ya gabatar da jawabi a kan munasabar ta Nisf Sha’aban.

Ana cikin gabatar da taron ne gamayyar jami’an tsaron ‘yan sanda (Police), soja (Army), DSS suka zo wajen cikin motoci sama da 50, inda suka tare ‘bakin shiga wajen taron, suka hana ‘yan uwan da suke zuwa shiga, inda wasu wasu ‘yan uwa suka tsaya a kofar wajen har zuwa lokacin da aka yi addu’a aka watse.

Jami’an tsaron sun zo da shiri na musamman ne, a yayin da wasu daga cikin su ke kokarin harzuƙa ‘yan uwa, wasun su suna ɗaukar Video, yayin da ‘yan uwa suka dauki matakan kaucewa tarkonsu ta hanyar sanya ido, da tattaunawa har aka tashi.

Ya zuwa lokacin hada rahoton nan, an ci gaba da yin taron a wani wurin a Abuja.

Jiya Alhamis ne aka fara gudanar da taron na Nisf Sha’aban a Abuja, inda aka gabatar da taron musamman, tare da majalisin mawaka.

Nisf Sha’aban rana ce mai daraja a Musulunci, a yayin da ta dace da ranar haihuwar jikan Manzon Allah (S), Imam Mahdi (AS) wanda shi ne limami na 12 a cikin halifofin da Manzon Allah (S) ya bar wa al’umma a bayansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *