Kisan ‘yan’uwa 4 a Muzaharar Ashura a Sakkwato:

Kotu ta umarci ‘yan sanda su biya diyyar Naira miliyan 80

Daga Wakilinmu

Kotun daukaka kara ta Tarayya da ke zamanta a Sakkwato ta umurci rundunar ’yan sandan Nijeriya su biya diyyar Naira miliyan 80 ga iyalan wasu ’yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky hudu, tare da raunata 12 da ’yan sandan suka kashe bayan kammala Muzaharar Ashura a Sakkwato a ranar 19/08/2021.

            ’Yan’uwa a karkashin Farfesa Ibrahim Mungadi sun shigar da kara ne suna neman a tilasta ’yan sanda su biya diyyar kisan gillar da suka yi wa matasan da ba su aikata laifin komai ba.

Rundunar ’yan sanda sun auka wa masu Muzaharar Ashura da harbi da harsasai masu rai a daidai lokacin da ake gudanar da jawabin rufe Muzaharar da ta shafe sama da awa ]aya da rabi ana gudarwa lami lafiya.

Harkar Musulunci ta saba shirya Muzaharar juyayin kisan gillar da aka yi wa jikan Manzon Allah (S), Imam Husaini (AS) a Karbala, Limamin Shi’a na uku daga cikin limaman shirya a Karbala a shekara ta 61 bayan hijira.

A baya dai wata babbar kotun Tarayya da ke Sakkwato ta yanke hukunci kan shari’ar, wanda ’yan Shi’a a jihar ba su gamsu da hukuncin ba, don haka suka ]aukaka }ara.

Hukuncin, wanda Mai Shari’a Mohammed Danjuma ya karanta a ranar Litinin, ya bayyana kisan da aka yi wa ’yan Shi’a a Muzaharar Ashura a matsayin ganganci, rashin gaskiya, rashin bin doka da oda.

Don haka kotun ta umurci wadanda ake kara a shari’ar (’yan sandan Nijeriya) da su biya diyyar Naira miliyan 10 ga kowanne iyalan mamacin.

Sannan kuma ta umurci ’yan sanda da su biya diyyar Naira miliyan biyu ga wasu makoki uku da suka samu raunuka a yayin harin.

Kotun ]aukaka }ara ta kuma umurci ’yan sanda da su biya ’yan Shi’a a jihar Sakkwato karin diyyar Naira miliyan 30 a kan bata mata lokaci da suka yi.

Wa]anda suka yi shahadar a harin na ’yan sanda sun hada da; Hassan Abubakar Sakkwato, Imrana Yabo, Muhammad Bello Illela da kuma Shahid Ali Haidar Bodinga wanda ya yi shahada bayan jinya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *