Hoto: Idris (na 4 daga hagu) tare da shugabannin Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE) a lokacin ziyarar
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga kafafen yaɗa labaran Nijeriya da kada su yi ƙasa a gwiwa wajen kare dimokuraɗiyyar ƙasar da aka kwashe shekaru 24 ana yi.
Ministan ya jaddada hakan ne a wata ziyarar ban girma da Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE) ta kai masa a ofishinsa domin tattaunawa kan shirye-shiryen Babban Taron Editocin Nijeriya (ANEC) karo na 20, wanda aka shirya gudanarwa a ranakun 6-9 ga Nuwamba, 2024, a Yenagoa, Jihar Bayelsa.
Idris ya jaddada muhimmancin rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen tallafawa tafiyar dimokuraɗiyyar Nijeriya, inda ya tuna da muhimmiyar rawar da suka taka a gwagwarmaya da mulkin kama-karya na sojoji.
“Kowa ya yi gwagwarmaya sosai a tafiyar dimokuraɗiyyar Nijeriya, inda kafafen yaɗa labarai ke kan gaba wajen yaƙi da mulkin kama-karya na soji.
“Saboda haka, shekaru 24 bayan haka, bai kamata a ga kafafen yaɗa labarai sun yi ƙasa a gwiwa ba a wannan muhimmin lokaci. Abin da ya kamata su yi shi ne ci gaba da ƙarfafa goyon bayansu ga dimokuraɗiyya.”
Ministan ya tabbatar wa shugabannin NGE, ƙarƙashin jagorancin Shugaban NGE, Eze Anaba, kan ƙudurin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kare martabar dimokraɗiyya, gami da ‘yancin yaɗa labarai.
Ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su zama jagororin kare dimokuraɗiyyar Nijeriya, da inganta zaman lafiya, haɗin kai, da tsaron ƙasa wajen yaɗa lamuran ƙasa.
Idris ya ci gaba da bayyana cewa ajandar kawo sauyi na gwamnatin Tinubu na ci gaba da gudana, ya kuma roƙi kafafen yaɗa labarai da su bayyana abubuwa masu kyau, yana mai cewa Nijeriya na kan hanyar zuwa wani sabon zamani na ci gaban zamantakewa da tattalin arziƙi, wanda ke zuwa da ƙalubale.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa ɓangaren yaɗa labarai ta hanyar ayyuka na musamman kamar bayar da lamuni ta Bankin Masana’antu da magance tsadar buga jaridu.
A nasa jawabin, Anaba ya bayyana muhimmancin taron ANEC da ke tafe a Jihar Bayelsa, inda ya bayyana cewa takensa, “Haɓaka Tattalin Arziƙi da Dabarun Ci Gaba a Ƙasa Mai Ɗimbin Albarkatu,” ya yi daidai da buƙatun da Nijeriya ke da shi a halin yanzu da kuma buƙatar neman mafita don samar da ci gaba.