Ma’aikatar lafiya da ke Gaza a ranar Alhamis ta bayyana cewa akalla mutane 29,410 aka kashe a yankin Falasdinawa yayin yaki a zirin.
Kamar yadda kafar watsa labaru ta The New Arab ta ruwaito, wani jawabin ma’aikatar ya ce mutane 97 suka rasa rayukansu a cikin awowi 24 da suka gabata, yayin da wasu 69,465 suka jikkata tunda yakin ya fara a ranar 7 ga watan Oktobar shekarar 2023.