Fulani makiyaya mutum hudu da aka bayyana sunansu da Abdul Juli, Sule Abubakar, Adamu Mato da Saidu Payo sun rasu a karamar hukumar Takum da ke jihar Taraba bayan ruwaito cewa sun dafa tare da cin kifin da suka tsinta a bakin ruwan rafin Kashimbila yayin da suke yin kiwo, kamar yadda rahoton PM News ya bayyana.
Shugaban karamar hukumar ta Takum da ke jihar Taraba, Honorable John Ali, ya tabbatar da faruwar al’amarin ga kafar watsa labaru ta jaridar Leadership.
Kamar yadda shugaban karamar hukumar ya bayyana, wasu mutum biyu (Yusuf Musa da Ibrahim Haruna) na kwance a asibiti biyo bayan al’amarin wanda ya faru a ranar 22 ga watan Fabrairun 2025 a wata al’umma da ke kusa da dam din da ake amfani da shi daban-daban na Kashimbila.
Ali ya bayyana cewa Fulani makiyayan ba su san cewa kifin da suka tsinta a bakin rafin na dauke da guba ba.
Kamar yadda ya shaida, Fulani makiyayan sun tsinci wani kalar kifi ne da ake kira “Frog Fish” wanda ya ke dauke da guba matuka, suka dafa suka ci.
Kamar yadda jaridar Leadership ta bayyana, Juli, Abubakar, Mato da Payo sun mutu ne nan take a wurin bayan sun ci kifin.
Sai dai, wasu makiyayan su biyu wadanda suma sun ci a yanzu haka suna samun kulawa a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba a Takum.