Masu garkuwa da Daliban Kaduna sun nemi a ba su naira biliyan 1 kudin fansa

Wadanda suka yi garkuwa da yaran makaranta a jihar Kaduna sun yi magana da kakakin iyalan wadanda suka kama, inda suka nemi a basu naira biliyan 1 (dalar Amurka 620,432) domin su sako yaran.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, Reuters ta ma bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun ma sha alwashin kashe daluban da ma’aikatan cikin kwanaki 20 idan ba a biya masu bukatarsu ba.

A ranar 7 ga watan Maci na shekarar 2024 ne ‘yan bindiga suka kai hari a al’ummar Kuriga a karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna tare da yin garkuwa da dalubai akalla 286 ciki har da wasu malamai a makarantar firamare ta LEA Kuriga.

A jiya shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya bayar da umarni ga jami’an tsaro da ma’aikatar tsaro cewa gwamnati ba za ta biya kudin fansa ga masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga ko kuma duk wasu masu aikata laifi ba domin a sako wadanda aka yi garkuwa da su.

Sai dai, rayuwar jwadannan dalubai ta shiga cikin rashin tabbas biyo bayan barazanar da kasa ta wayi gari da ita daga wajen masu garkuwa da mutanen.

Masu garkuwa da mutanen kamar yadda Jubril Aminu, wani shugaban al’umma wanda ya ke a matsayin kakakin iyalan wadanda aka yi garkuwa da su, ya ce: “Sun nemi a ba su kudi (naira) biliyan 1 daidai a matsayin fansa ga duka kananan daluban, manyan daluban da ma’aikatan makarantar.” A cewar Aminu.

“Sun bayar da wa’adin biyan fansar kwanaki 20, wanda zai fara daga ranar da aka yi garkuwar. Sun ce za su kashe duka daluban da ma’aikatan idan ba a biya abunda suka bukata na fansar ba.”

Idris Ibrahim, wani jami’i zababbe daga mazabar Kuriga, ya tabbatar da yawan kudin da aka nema domin fansar.

“E, masu garkuwa da mutanen sun kira al’ummar ta hanyar nambar wayar Jubril Aminu inda suka nemi hakan.” A cewarsa.

“Sun kira da boyayyar namba wadda hukumomi ke aiki domin gano nambar.” Kamar yadda Ibrahim ya shaidawa Reuters.

Ya kara da cewa jami’an tsaro suna daukar “cikakkun matakan da suka dace” domin tabbatar da sakin daluban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *