Mata ‘yan kasuwan Osun sun yi gargaɗi: In mun ga Tinubu, za mu yi masa duka saboda wahala

Wasu mata ‘yan kasuwa a jihar Osun sun yi kira da shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya sauka daga kan muƙaminsa sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da wahala a ƙasa.

Mata ‘yan kasuwan, waɗanda suka yi suka cikin fushi ga gwamnatin Tinubu, sun yi barazanar yi masa duka inda za su gan shi ido-da-ido, kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Mata ‘yan kasuwan sun bayyana haka ne ga wani mai rahoton labaru a wani bidiyo, wanda Sahara Reporters ta gani a ranar Laraba. Sun bayyana cewa Tinubu ya ba ‘yan Nijeriya kunya, musamman Yarbawa.

Wata babbar mata ta bayyana cewa, “Ya ba mu kunya a ƙasar Yarbawa, ba ya ɗabi’u kamar Bayarbe.”

Wata kuma ta ce, “Komai ya yi tsada, har ta kai ga matakin da ba za mu iya sayen kwanon gari ba. Mun gaji da komai, lokacin da na fara kasuwanci, katan ɗin kifi naira 200 ne, amma yanzu naira 20,000 ne.

“Ba mu da abincin da za mu ci, tsofaffin mutane na mutuwa. Kasuwanci ba ya tafiya, kuma babu komai. Duk muna jin yunwa.

“Wannan matsalar ta yi yawa. Idan ba za ka iya warware matsalarmu ba, kada ka ƙara mana.”

Wata ‘yar kasuwar ta roƙi shugaban ƙasar da ya tausaya wa ‘yan Nijeriya, “Mun gaji da Nijeriya, komai ya yi tsada, komai na ƙara tsada a kullum.”

“Abinda ya yi mana alƙawari ba shi ke faruwa yanzu ba. Wannan ya yi yawa. A wannan matakin mun gaji. Abubuwa sun yi tsada da yawa. Katan ɗin Titus naira 100,000; a da naira 17,000 ne. Kote ya kusa naira 60,000. Shawa, wanda muke sayarwa a kan naira 70, yanzu ya ƙaru zuwa naira 700.”

Yayin da aka tambaye su me za su faɗa wa shugaban ƙasa, inda za su samu damar ganin sa, sai ɗaya daga cikin ‘yan kasuwar ta ce, “Za mu doki shugaban ƙasar inda za mu samu damar ganin sa, za mu doke shi. Abin da ya faɗa mana ba shi yake yi ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *