Hukumar samar da abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta dakatar da kai kayyakin abinci zuwa jihar Gezira na wani ɗan lokaci, kwanaki bayan da dakarun RSF suka ƙwace iko da birnin Wada Madani.
Shugaban hukumar WFP a Sudan, Eddie Rowe cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce wajen mafaka a yanzu ya zama fagen daga lamarin da yake da mummunan tasiri a kan farar hula.
“Hakan ya tilasta WFP tsagaita shigar da kayayyakin abinci zuwa wasu wurare a jiharGezira daidai lokacin da mutane suka fi bukatar agaji.”
An yi ƙiyasin mutum 300,000 ne suka tsere wa rikici a jihar tun Juma’ar da ta gabata, kamar yadda hukumar ta bayyana.
WFP ta daɗe tana samar da agajin abinci ga mutum 800,000 a Gezira da waɗanda suka ɗaiɗaita sakamakon yaƙi a Khartoum, babban birnin Sudan.
Akwai fargabar soma yaƙi a Gezira na iya ta’azzara matsalar jin ƙai a Sudan.