Minista Alake na cimma nasarori wajen sauya fasalin sashen ma’adinai, inji Idris

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris (a dama), tare da Ministan Ma’adinai, Mista Henry Dele Alake, wanda ya kai wa ziyarar aiki a ranar Alhamis a Abuja

 
MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yaba wa takwaran sa na Ma’adinai kan abin da ya kira “manyan matakan cigaba da ake samu a Ma’aikatar Ma’adinai da ake ɗauka don kawo sauyi a fagen a matsayin sa na wanda ke sahun gaba na muradun tattalin arzikin Nijeriya.”
 
A cikin wata sanarwa, Malam Rabi’u Ibrahim, wato mataimaki na musamman ga ministan kan harkokin yaɗa labarai, ya ce Idris ya faɗi haka ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki ga Ministan Ma’adinai, Mista Henry Dele Alake, a ranar Alhamis a Abuja.
Ministan ya yi la’akari cikin gamsuwa da cewa ayyuka masu tasiri a fagen ma’adinai waɗanda ke bada sakamako a kyakkyawan sauye-sauye da ake matuƙar buƙatar su da canza muradu, wanda ya yi daidai da manyan manufofin Renewed Hope Agenda ta gwamnatin Tinubu.
 
A cewar Idris, Mista Alake ya na dasa ginshiƙan gudanarwa waɗanda ba a saba ganin irin su ba a sashen ma’adinai sannan su na haifar da kyakkyawar fata a zuciyar ‘yan Nijeriya game da gina ƙasa mai ƙarfin tattalin arziki. 
 
Ya bayyana ziyarar tasa ga Alake a matsayin ziyarar aiki ta farko da ya kai wa wani takwaran sa minista, ya na faɗin cewa Alake mutum ne wanda ya samu sani daga sassa daban-daban, kuma mai basirar cimma nasara a wani sashe da ya kusa durƙushewa, wanda zai ƙarfafa hanyoyin kuɗin shiga na Nijeriya ya kuma faɗaɗa damar ɗaukar ma’aikata.
 
Shi kuma Mista Alake sai ya ce shi da Idris sun daɗe su na hulɗar siyasa tare, kuma Idris mutum ne wanda ya yi amanna da ƙudirorin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, musamman wajen abin da ya dace da tattalin arziki da zamantakewar Nijeriya baki ɗaya, ta hanyar Renewed Hope Agenda.  
 
Ya ce: “Idris da ni abokai ne kuma wannan ziyarar ta na alamta burin mu na ciyar da ƙasar nan gaba domin ta zama mai faɗaɗan hanyoyin tattalin arziki kuma mu jawo hankalin duniya zuwa ga sashen ma’adinai a matsayin hanyar jawo wa Nijeriya Jari Kai-tsaye daga Waje, wato ‘Foreign Direct Investment’ (FDI).”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *