Minista Hannatu Musawa ta ƙudiri aniyar kafa Gidan Tarihi da Gidan Wasanni na Ƙasa a Abuja

Barista Hannatu Musa Musawa (ta farko daga dama) tare da jami’an ma’aikatar ta a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa a ranar Alhamis

* Ta yi kukan ƙanƙantar Kasafin Kuɗin ma’aikatar ta
Ma’aikatar Fasaha, Al’adu Da Tattalin Arzikin Basira ta ƙudiri aniyar kafa Gidan Tara Kayan Tarihi da kuma Gidan Wasanni a Unguwar Basira da za a yi a Abuja.
Ministar ma’aikatar, Barista Hannatu Musa Musawa, ita ce ta bayyana hakan a lokacin da ta gabatar da Kasafin Kuɗin ma’aikatar na shekarar 2024 a gaban Kwamitin Fasaha, Al’adu Da Tattalin Arzikin Basira na Majalisar Dattawa a ranar Alhamis a Majalisar Tarayya a Abuja.
A cikin sanarwar da Hadimar ta ta Musamman kan Yaɗa Labarai, wato Nneka Ikem Anibeze, ta fitar, an ruwaito Barista Hannatu ta na cewa kafa wuraren guda biyu ya na daga cikin manyan muhimman ayyukan da ma’aikatar ta sanya a gaba da nufin samar da aikin yi, ba kurum ga masu ayyukan fasaha ba har ma ga sauran ‘yan Nijeriya baki ɗaya.
A cewar ministar, cimma wannan nasarar zai yiwu ne idan har an samu amincewa da Kasafin Kuɗin shekarar 2024 daga Majalisar Dattawa.
Haka kuma ministar ta yi la’akari da cewa kuɗin da aka kasafta wa ma’aikatar ta sun yi kaɗan matuƙa, sannan ta yi kira ga Kwamitin na Majalisar Dattawa da ya ƙara yawan kuɗin a cikin Kasafin shekarar 2024 ɗin.
Barista Hannatu ta ce: “Kuɗin da aka kasafta wa Ma’aikatar sun yi kaɗan matuƙar gaske, wanda ya sa ba za mu iya cimma wani abin a zo a gani ba idan ba a bada kuɗin da su ka dace ba.
“Nasarar da wannan Ma’aikatar za ta cimmawa gagaruma ce idan mun yi abin da ya kamata, don haka mu na so mu ga abin da za mu iya yi a matakin majalisa domin bai wa ma’aikatar irin kasafin kuɗi da ya kamata tare da goyon bayan da mu ke buƙata don cimma burin mu a tsarin da gwamnati ta yi, wato domin mu cimma muradun Sabuwar Alƙiblar Saisaita Ƙasa ta mai girma Shugaban Ƙasa.”
A bisa Sabuwar Alƙiblar Saisaita Ƙasa ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu dai, wannan ma’aikatar ta ƙudiri aniyar kawo gudunmawar kuɗin shiga da ya kai naira biliyan 100 ga tattalin arzikin ƙasar nan zuwa shekarar 2030 tare kuma da kafa manyan ayyuka da su ka haɗa da gina Gidan Wasanni na Ƙasa da Gidan Tara Kayan Tarihi na Ƙasa a birnin Abuja, da sauran su.
Tun da farko, sai da Barista Hannatu Musa Musawa ta nanata aniyar ma’aikatar ta ta sake fasalin Nijeriya ta hanyoyin waɗannan ayyukan da ta ke son ta aiwatar.
Ta yi bayani kan muhimmanci da alfanun da ke tattare da Tattalin Arzikin Basira da kuma gundarin ayyukan da aka rataya wa Ma’aikatar waɗanda su ka haɗa da janyo zuba jari, haɓaka al’adu da adana su, da sauran su, kamar yadda sashe na 21 na Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ya tanadar.
Ta ce, “Mun lissafa Alamomin Manyan Nasarorin da ma’aikatar ta ke so ta cimmawa kuma a shirye mu ke mu ga mun cimma dukkan nasarorin da mu ka ɗora wa kan mu.
“Wannan sabuwar ma’aikata ce wadda kuma ta ke so ta yi ƙoƙarin samar da aikin yi sannan kuma ta samar da Tsarin Kare Haƙƙin Mallaka wanda zai kula da sha’anin al’adu da ƙirƙira a Nijeriya. Saboda haka, wannan abu ne wanda ke buƙatar cikakkiyar ɗaukar nauyi ta fuskar kuɗi.”
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Fasaha, Al’adu Da Tattali Arzikin Basira na Majalisar Dattawa, Sanata Mohammed Ogoshi Onawo, ya yaba wa ministar saboda sababbin al’amuran da ta bijiro da su, wato kafa Gidan Tara Kayan Tarihi da kuma Gidan Wasanni a Abuja, kuma ya bayyana cewa sake duba kasafin kuɗin zai taimaka mata wajen gudanar da aikin ta da kyau kuma ta cimma burukan ma’aikatar.
Ya ce: “Wannan kwamiti zai so mu riƙa haɗuwa da juna a kai a kai a cikin shekara da za a yi nan gaba domin a samu daidaito kuma a tabbatar da haɗin gwiwa da Majalisar Dattawa.”
Wani memba a kwamitin, Sanata Ede Dafinone, mai wakiltar Mazaɓar Delta ta Tsakiya, shi ma ya yi tsokaci kan ƙanƙantar kasafin kuɗin, ya bayyana damuwa kan yadda ma’aikatar za ta iya aiwatar da manyan ayyuka da wannan ɗan cikin cokalin kasafin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *