Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ba da umarnin kafa wani kwamiti mai mutum biyar da zai fito da tsarin aiki da Hukumar Naƙasassu ta Ƙasa domin wayar da kan jama’a game da ‘yanci da kuma damarmakin naƙasassu.
Ministan ya bayar da umarnin ne a Abuja a ranar Laraba a lokacin da ya karɓi baƙuncin Babban Sakataren Hukumar Nakasassu, Dakta James Lalu, a wata ziyarar ban-girma da ya kai ofishin sa.
Ya ce: “Daga yau, za mu kafa kwamitin da zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ku don duba takamaiman buƙatun ku domin mu taimaka wajen ganin an cimma manufofin ku.”
Idris ya ƙara da cewa zai ba hukumar damar yin aiki da hukumomin yaɗa labarai da kayan aikin ma’aikatar sa domin kare haƙƙi da mutuncin naƙasassu da kare su daga wariya.
Ministan ya ce Shugaba Tinubu ya yi imani da haɗin kan jama’a, don haka ya jajirce wajen ba da ganuwa, karɓuwa, da alhaki ga naƙasassu a gwamnatin sa.
Ya ƙara da cewa, “Babu wani ɓangare na al’ummar Nijeriya da za a bari a baya a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.”
Ya yi alƙawarin jagorantar kai shawarwari ga gwamnonin jihohi game da tsarin doka na naƙasa a jihohin su.
A nasa jawabin, Dakta Lalu ya ce ya je ma’aikatar ne domin neman haɗin gwiwa domin wayar da kan jama’a kan haƙƙin naƙasassun.
Ya ce wasu sassan Dokar Naƙasa sun umurci masu ba da sabis da su samar da dama ta musamman ga naƙasassu a wurare kamar gine-ginen jama’a, sufuri, da wuraren kula da lafiya da sauran su ba tare da nuna wariya ba.
Dakta Lalu ya ce naƙasassu na da ɗimbin damarmaki waɗanda suka haɗa da fasahohi daban-daban, cancanta, da basirar da ake buƙata don cigaban tattalin arzikin ƙasa.