Hoto: Idris (na 3 daga hagu) da Ribadu (na 3 daga dama) tare da iyalan da aka sace
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi maraba da sakin wasu ‘yan jarida biyu da aka sace daga gidajen su da ke bayan garin Kaduna a ƙarshen makon jiya.
Da yake jawabi a lokacin da ya karɓi baƙuncin ‘yan jaridun biyu, wato AbdulGafar Alabelewe na jaridar The Nation da AbdulRaheem Aodu na jaridar Blueprint, daga Mai Bai Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ministan ya yaba wa hukumomin tsaro bisa gaggawar ceto waɗanda lamarin ya shafa.
An saki ‘yan jaridar biyu tare da matar Mista Alabelewe da ‘ya’yan sa biyu.
Idris ya jajanta wa iyalan biyu, inda ya ce, “Muna matuƙar godiya da abin da kuka yi. Muna sane da cewa wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarin da kuke yi na ganin an kuɓutar da duk waɗanda aka sace tare da sake haɗa su da iyalan su.
“Ina kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da yin imani da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da hukumomin tsaro.”
Ya ƙara da cewa, “Hukumomin tsaron, a ƙarƙashin inuwar NSA, suna aiki tuƙuru domin ganin an kuɓutar da duk waɗanda aka sace ba tare da biyan kuɗin fansa ba.”
Da yake magana tun da farko, Malam Ribadu ya ce an ceto mutanen biyar da aka sace ne sakamakon haɗin gwiwar da hukumomin tsaron suka yi wanda ya kai ga gudanar da bincike da ceto cikin gaggawa.
Da yake mayar da martani, ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto, Mista Alabelewe, ya gode wa Ribadu da tawagar sa bisa gaggawar da suka yi.
Ya ce, “Aikin ceton da ya fitar da mu daga cikin daji a jiya ya ba mu fata a ƙasar mu kuma ya ba mu ƙwarin gwiwar yarda da cewa gwamnati da gaske take wajen ganin ta magance wannan matsalar ta garkuwa da mutane.
“Ban taɓa tunanin cewa nan da mako guda da sace mu za mu kuɓuta ba. Muna godiya da gwamnati ta ɗauki mataki kuma ta tabbatar an sake mu.”