Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Mohammed Umar Bago, murnar cikar sa shekara 51 a duniya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Idris ya yaba wa gwamnan bisa shugabancin sa da kuma jajircewar sa wajen ganin cigaban Jihar Neja.
Ya ce: “Gwamna Bago ya nuna ƙwarewa ta musamman a shugabanci, hangen nesa da kuma jajircewa wajen cigaban Jihar Neja, ta hanyar aiwatar da manyan shirye-shiryen da ke inganta rayuwar al’umma.
“Jajircewar sa ga haɓaka ababen more rayuwa, noma da ƙarfafa matasa yana ci gaba da mayar da Jihar Neja abin koyi wajen cigaba da wadata.”
Ministan ya ce yana taya gwamnan na jihar su murna, yana mai bayyana shi a matsayin jagora mai kishin hidimta wa al’umma da cigaban ƙasa.
Idris ya ƙara da cewa, “Yayin da yake bikin wannan rana ta musamman, ina taya shi murna a matsayin jagora wanda jajircewar sa ga hidima da shugabanci ke nuna ainihin cigaba.
“Ina roƙon Allah ya ci gaba da ba shi lafiya, hikima da ƙarfi don ya ci gaba da tafiyar da Jihar Neja zuwa matakai mafi girma.”
Ya kammala da taya Gwamna Bago murna, inda ya ce, “A karo na biyu, muna taya ka murna da fatan alheri a wannan rana mai albarka, Mai Girma Gwamna!”