Ministan Yaɗa Labarai ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su dawo da kyawawan ɗabi’un da suka rasa

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su dawo da kyawawan ɗabi’un da suka rasa tare da ci gaba da addu’o’in samun zaman lafiya da cigaban shugabannin mu da ƙasar mu.

Ya yi wannan kiran ne a Kaduna bayan kammala Sallar Idi.

An gudanar da sallar ne a makarantar Kaduna Capital da ke Kaduna a ranar Laraba.

Ministan ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu addu’a, tare da amincewa da ƙoƙarin da yake yi na mayar da Nijeriya cikin ƙasashe mafiya inganci a duniya.

Ya ce: “Ana farfaɗo da tattalin arzikin mu, kasuwar canjin kuɗaɗen waje na daidaituwa, ana kuma farfaɗo da harkar noma ta yadda za a samu wadatar abinci ga jama’ar mu. Haƙiƙa yanayin tsaron ƙasar nan ma yana inganta.”

Idris ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi Allah wadai da duk wasu munanan ayyuka da ‘yan ta’adda ke aikatawa, tare da fatan za su tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya sun zauna lafiya.

Haka kuma ya bayyana damuwar sa kan yadda a hankali ɗabi’un ‘yan Nijeriya ke taɓarɓarewa tsawon shekaru.

Ya yi kira ga dukkanin mu da mu haɗa kai mu dawo da waɗannan ɗabi’u domin farfaɗo da kan mu da ƙasar mu.

Ya kuma buƙaci matasa da su koyi darasi daga abubuwan da suka faru da dattawan su, kuma su guji biye wa sababbin yayi da duniya ke ciki.

“Nijeriya babbar ƙasa ce; Abin da ya kamata mu yi shi ne mu haɗa kai mu tabbatar an rungumi dukkan kyawawan ɗabi’u domin amfanin Nijeriya,” inji shi.

Ministan ya ƙara da cewa: “Domin Nijeriya ta sake zama babbar ƙasa, dole ne mu canza ɗabi’un mu kuma mu ci gaba da nuna duk wasu ɗabi’u da muka koya a cikin watan Ramadan.”

Babban limamin masallacin Makarantar Capital, Imam Abdurrahman, wanda ya jagoranci sallar, ya gabatar da huɗuba, inda ya yi kira ga Musulmi da Kiristoci da su tabbatar da cewa Nijeriya ta zauna lafiya da haɗin kai.

Shi ma ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su dawo da waɗancan ɗabi’u domin su farfaɗo da ƙasar mu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *