“Avian influenza” a turance wadda aka fi sani da murar tsuntsaye, ta kashe tsuntsaye 300 a wata gona da ke jihar Filato.
Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, babban jami’in kula da dabbobi na jihar, Dakta Shase’et Sipak, ne ya bayyana haka ga kamfanin dillancin labaru na Nijeriya (NAN) a ranar Laraba a Jos.
Sipak ya bayyana cewa cibiyar binciken dabbobi ta kasa (NVRI) da ke Vom a jihar Filato ta tabbatar da barkewar.
Ya ma shaida cewa gonar da abin ya shafa tana a karamar hukumar Bassa ne da ke jihar.
“Yayin da muka samu labarin zargin barkewar a Bassa, nan da nan muka tafi muka dauki dan wani sashe domin gwaji inda daga baya dakin binciken NVRI ya tabbatar.”
“Masu dauke da cutar suna da ita ne kashi 100 cikin 100; a cikin tsuntsaye 300, sama da 280 sun mutu. Daga baya sai muka rage yawan wadanda suka ragu.
“Mun ma rufe gonar tare da daukar wasu matakai da ke da nufin hana yaduwar kwayoyin halittu masu cutarwa domin hana yaduwar cutar zuwa wasu gonakin.” Kamar yadda ya bayyana.
Sipak ya yi kira ga masu kiwon tsuntsaye a jihar da su dauki kwararan matakai na hana kwayoyin halittu masu cutarwa yaduwa domin hana yaduwar cutar da kuma tseratar da tsuntsayensu.”