Muzaharar goyon bayan Palasdinawa: ‘Yansanda sun kashe 2 a Kaduna

Shahid Sidi Anas

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, an tabbatar da cewa rundunar ’yansanda ta jihar Kaduna ta kashe ’yan’uwa musulmi almajiran Shaikh Zakzaky biyu da suka fito muzaharar nuna goyon baya ga Palasdinawan da Isra’ila ke yi wa ruwan bama-bamai a kulluma tana kashewa.
Da misalin karfe 11 na safiyar Ranar Alhamis 16/11/2023 (2/5/1445) ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky a Kaduna, suka fita Muzaharar nuna goyon baya ga raunanan al’ummar Palasdinawa da Yahudawan Isra’ila ke kashewa.

Shahid Muhsin Abubakar 

Muzaharar wacce ta kunshi mata da kananan yara, an faro ta ne daga Nepa Roundabout da ke tsakiyar garin Kaduna, ta isa gaban ofishin Hukumar kare hakkin ɗan Adam (Human Right Commission), sai ga jami’an ‘yan sandan Mopol nan.
Suna zuwa suka fara bude wuta, da harbi da bindiga da Tiyagas, inda suka jikkata gomomin ‘yan’uwa, a yayin da biyu daga ciki zuwa yanzu suka yi shahay sakamakon harbin.
Shahidan su ne; Shahid Sidi Anas Kaduna, wanda matashi ne dan kimanin shekaru 30, yana da mata da yarinya daya, sai kuma Shahid Muhsin Abubakar, wanda shi yaro ne dan kimanin shekaru 15 da haihuwa.

Ml. Tirmizi, Wakilin ‘yan’uwa musulmi na Kaduna

A yayin Muzaharar, yan’uwa mata sun rike abubuwan da ke alamta jariran Palasdinawa da Isra’ila ke kashewa a tsakanin nan, musamman a hare-haren da Haramtacciyar ƙasar Isra’ila din ke kaiwa a yankin Gaza a asibitoci, makarantu da gidajen al’umma, wanda yau kimanin kwanaki 40 kenan ana cikin wannan halin.
Hoto: Shahid Sidi Anas sanye da koren kyalle a wuya
Hoto: Shahid Muhsin Abubakar sanye da kyallen Kudus a wuya.
Hoto: Wakilin ‘yan’uwa musulmi na Kaduna, Mal. Tirmizi a tsakiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *