Hukumar da ke sa ido a kan abinci da magungunan ta Nijeriya (NAFDAC) ta kulle shaguna 3000 a Idumota Open Market da ke Legas a makon farko na gudanar da ayyukan ta.
Kamar yadda Channels ta ruwaito, kamar yadda wani jawabin hukumar a shafin X ya bayyana, hukumar a yayin kutsen jami’anta sun binciko karya ka’idoji na ban mamaki, ciki har da magungunan rigakafi da aka ajiye a wuraren da suka lalace, dakunan da ba iska a ciki rurrufe da karafuna wanda hakan babban hatsari ne ga lafiya.
An ma gano magunguna masu hatsari da aka haramta amfani da su masu yawa, ciki har da allurar Analgin, magungunan rage radadin cutar HIV da ake bayarwa kyauta da aka karkatar da su, da magungunan da suka tashi daga aiki da ake shirin dawo da su domin a amince da su.
“A makon farko na tabbatar da bin doka, NAFDAC ta yi bincike tare da rufe shaguna sama da 3000 a Idumota Open Drug Market da ke Legas.
“A cikin abubuwan da aka gano har da magungunan rigakafi da aka ajiye a wuraren da suka lalace, dakunan da ba iska a ciki rurrufe da karafuna a inda ba tsafta kwata-kwata.
“Bayan haka, an gano magunguna masu yawa da aka haramta amfani da su, ciki har da allurar Analgin, magungunan rage radadin cutar HIV da ake bayarwa kyauta wadanda aka karkatar da su da kuma magungunan da sun tashi daga aiki wadanda ake shirin sake dawo da su domin a sake amincewa da su da wuraren sayar da magani da ba a yiwa rijista ba.
“Mun kwashe magungunan da ba kan ka’ida suke ba da suka kai cikin manyan motoci 12. Fakiti da ba komai a ciki da katan-katan na allurar maganin Maleriya da suka tashi daga aiki an same su a wani shagon da ake ajeye abubuwa. Kananan kwalaben sa magunguna na ruwa duk an fitar da su.
“HappeningNow Ecstasy (MDMA ko Molly), maganin tari na ruwa na “Codeine” kala-kala da Tramadol 225, duk an gano su a wani gidan ajiye kayayyaki a cikin kasuwar nesa da bangaren da ake sayar da magunguna inda ake sayar da sauran.”