Nijeriya na da ‘yan kurkuku sama da 48,000 da ke jiran yanke hukunci – NCoS

Daga Abubakar Musa

Sama da ‘yan kurkuku 48,000 a Nijeriya masu jira a yanke masu hukunci ne (ATPs), kamar yadda Sylvester Nwakuche, mai rikon kwarya a hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Nijeriya (NCoS) ya bayyana.

Kamar yadda kafar watsa labaru ta Sahara Reporters ta ruwaito, Nwakuche ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da manyan jami’ai a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa, “A yanzu haka, kididdigarmu ya zuwa yau, 6 ga watan Janairun 2025, ta nuna cewa akwai mutane 48,932 da ke a tsare suna jiran hukunci (ATPs).” Kamar yadda ya bayyana.

Ya jaddada cinkoso a matsayin babban kalubale da ke fuskantar hukumar ta NCoS. “Cinkoso, ba tare da kokwanto ba, ya yi zarra a matsayin babban kalubalen NCoS.” A cewarsa.

Domin warware matsalar, Nwakuche ya bayyana shirye-shiryen hadin gwiwa da Antoni-Janar na kasa kuma ministan shari’a, Lateef Fagbemi, SAN, shugaban ‘yan sanda na kasa da sauran hukumomin yanke hukunci domin sa yanke hukunci ya yi sauri.

Ya ma yi bayani dangane da kokarin daukar matakan da ba sai an tsare mutum ba, sakin mutane da wuri da kuma gina sabbin wuraren tsare mutane na zamani masu daukar mutane 3000.

“Wannan gwamnatin za ta yi amfani da damarmakin matakan da ba sai an tsare mutum ba za su bayar domin rage cinkoson jama’a a gidajen kurkukunmu.” A cewarsa.

Ya bukaci jami’ai da ke wurare daban-daban da su hada hannu da alkalai da manyan masu shari’a wajen ganin ana yanke hukunci ba tare da bata lokaci ba.

“Ina bukatar da ku je wuraren alkalai na jiha, Antoni-Janar na jihohinku da sauran masu ruwa da tsaki a kan wannan al’amarin; wasunsu na bukatar a ilimantar da su a kan haka.” A cewarsa.

Nwakuche ya tabbatarwa masu ruwa da tsaki cewa za a mayar da hankali a kan shari’o’in da ba za a iya yi masu beli ba kamar fashi da makami da kisa wadanda sune ke da kashi 60 cikin 100 na wadanda ke jira a yanke masu hukunci (ATPs).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *