Nijeriya za ta ƙarfafa alaƙa da Indonesiya a taron ƙasar da Afirka karo na biyu

Gwamnatin Nijeriya za ta ƙarfafa hulɗar da ke tsakanin ta da Indonesiya yayin da aka fara taron ƙasar da nahiyar Afirka karo na biyu a birnin Bali na ƙasar Indonesiya.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, wanda yanzu haka yake Indonesiya domin wakiltar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban Tawagar Nijeriya a taron wanda, shi ne ya faɗi haka.

Ana gudanar da taron daga ranar 1 zuwa 3 ga Satumba, 2024.

Taken taron, “Bandung Spirit for Africa’s Agenda 2023” kwatankwacin taron Asiya da Afirka ne mai tarihi na 1955 da aka fi sani da “Taron Bandung”, wanda Indonesiya ta shirya, wanda ya nuna wani sabon babi na haɗin kai da haɗin gwiwa a cikin alaikar da ke tsakanin nahiyoyin biyu.

Taken kuma yana da nufin zurfafa haɗin gwiwa tsakanin Muradin Indonesiya na 2045 da Ajandar Tarayyar Afirka ta 2063.

Nijeriya da Indonesiya dai suna da alaƙa mai ƙarfi tsawon shekaru, wanda tun a shekarar 2022 gwamnatin Indonesiya ta ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da za ta zuba jari a cikin ta a nahiyar Afirka, matakin da ke nuna amincewar ƙasar da ƙarfin tattalin arzikin Nijeriya.

Adadin cinikayyar da ke tsakanin ƙasashen biyu ya kai dala biliyan 6 a 2023, wanda ya ƙaru daga dala biliyan 4 shekaru goma da suka gabata.

Bugu da ƙari, tallafin da Indonesiya ta bai wa Nijeriya ya haɗa da ba da gudunmawa a 2023 ta allurar rigakafi ta Pentavalent miliyan 1.58, wadda darajar ta ta kai kusan dalar Amurka miliyan 2, wanda ya kasance muhimmi wajen kare yaran Nijeriya daga cututtuka masu barazana ga rayuwa.

Yayin da yake Indonesiya, Minista Idris zai bayyana damarmakin saka hannun jari a Nijeriya a ɓangarori daban-daban da kuma bayyana nasarorin da aka samu na zamantakewa da tattalin arziki na Ajandar Sabunta Fata ta Shugaba Tinubu.

Zai kuma nemi a bai wa ‘yan kasuwa na Nijeriya damarmakin da za su shiga cikin tattalin arzikin Indonesiya.

“Ina fatan in wakilci Mai Girma Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwamnati da al’ummar Nijeriya a taron Indonesiya da Afirka karo na biyu, da kuma taron da zai zama wani muhimmin abin tunawa a cikin tafiyar ƙarfafa alaƙa tsakanin Indonesiya a ɓangare ɗaya da Nijeriya da Afirka a ɗaya ɓangaren,” inji Idris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *