Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana ƙudirin ma’aikatar sa na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin ƙasar Amurka domin inganta ‘yancin manema labarai a Nijeriya.
Rabi’u Ibrahim, mai taimaka wa ministan kan harkokin yaɗa labarai, ya faɗa a takardar da ya rattaba wa hannu cewa Idris ya faɗi hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan bayan ya yi wani zama da Jakaden Amurka a Nijeriya, Mista Richard Mills, a ofishin sa da ke Abuja a ranar Laraba.
Ministan ya ce: “Jakaden ya yi magana kan waɗansu abubuwa da yake ganin ya dace mu kula da su don inganta ‘yancin ‘yan jarida, mu kuma mun ba shi tabbaci kan irin abubuwan da muke yi, kuma ya ce ya san cewa muna yin abin da ya dace wajen tabbatar da cewa aikin jarida a Nijeriya ba kurum yana da cikakken ‘yanci ba ne, a’a har ma za a iya cewa yana daga cikin waɗanda suka fi ko’ina samun ‘yanci a faɗin duniya.
“Na san cewa akwai wasu ‘yan matsaloli nan da can, kuma muna aiki don kulawa da irin waɗannan wuraren don dukkan mu mu ci moriyar abin da ake kira ‘yancin aikin jarida, wanda muhimmi ne a kowace ƙasa mai da’awar mulkin dimokiraɗiyya mai ƙarko.”
Ministan ya nanata yadda gwamnatin Tinubu ta ba ‘yancin ‘yan jarida muhimmanci kuma ya tabbatar da cewa za ta ci gaba da inganta ‘yancin manema labarai a ƙasar.
Ya ce sun kuma tattauna kan yadda za su haɗa kai su yi aiki tare wajen yaƙar baza labaran bogi da na ƙage a ƙasar.
Ya ce: “Ya yi magana kan labaran bogi da na ƙage da na ƙarya, duk waɗannan abubuwan mun tattauna kan su. Dukkan mu mun yi amanna da cewa babu yadda za a yi ka gina al’umma ingantacciya a yayin da kake yaɗa labaran ƙarya kuma ba ka ɗauki batun labaran bogi da na ƙage da gaske ba.”
A nasa jawabin, Jakada Mills ya ce zaman da suka yi da ministan sun yi shi ne domin su tattauna kan hanyoyin ƙarfafa dangantakar da ke akwai tsakanin gwamnatin Amurka da ma’aikatar, musamman abin da ya shafi ‘yancin ‘yan jarida da haƙƙoƙin manema labarai.
Ya yi la’akari da ƙoƙarin da ministan ke yi wajen haɓaka ‘yancin ‘yan jarida da haƙƙoƙin manema labarai a Nijeriya.
Jakaden na Amurka ya yi la’akari da babban ƙalubalen da matsalar baza labaran bogi ke janyowa, musamman ga ƙasashen da ke tafiyar da mulkin dimokiraɗiyya a faɗin duniya.
Ya ƙara da cewa sun kuma yi musayar ra’ayi da shawarwari kan yadda za a magance ƙalubalen.