Shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Juma’a ya yi ikirarin cewa yanzu farashin abinci ya sauka, wanda hakan ya samar da sauki ga Musulmi masu gabatar da azumin watan Ramadan a yayin da ake tsaka da fuskantar hauhawar farashin kayayyaki da hargitsi a da tattalin arzuki wanda tsare-tsaren mulkinsa ya haifar.
Tinubu, wanda cire tallafin man fetur da ya yi da kuma rage darajar naira ya jefa miliyoyin ‘yan kasa cikin talauci mai zurfi, ya dage kan cewa “tsare-tsaren shi da matakan shi gabagadi na kawo sauyi” sun fara nuna sakamako mai kyau, kamar yadda kafar watsa labaru ta Sahara Reporters ta ruwaito.
Shugaban ya bayyana cewa tattalin arzukin kasa na cikin gida na Nijeriya (GDP) ya karu kuma kayayyakin abinci da ake bukata yanzu ana iya sayensu.
“Kayayyakin abinci da a da ke da farashi mai yawa yanzu suna sauka, wanda hakan ke samar da sauki ga al’ummarmu da ke azumi da dukkanin ‘yan Nijeriya.” Tinubu ya bayyana, duk da rahotanni masu yawa kan hauhawar talauci da kuma tsadar abinci a fadin kasa.
Shugaban kasar ya yi kalaman ne a wani sakonsa ga al’ummar Musulmi, inda ya neme su da su rungumi tarbiyyar da kan su da kuma taimako a yayin wata mai tsarki na Ramadan.
Ya ma tabbatarwa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatinsa za ta kara dagewa wajen kara yawan samar da abinci da kuma tabbatar da an wadatu.
“A yayin da lokacin damina ke kara gabatowa, muna nan kan kokarinmu na kara yawan samar da abinci da kuma wadatar abinci ga ‘yan Nijeriya.” Kamar yadda ya bayyana.
Sai dai, kamar yadda kafar ta Sahara Reporters ta ruwaito, ikirarin na Tinubu ya kasance daban da abinda ke a zahiri, domin ‘yan Nijeriya na cigaba da fuskantar wahalhalun da tsare-tsaren tattalin arzukin shi suka haifar.
Tun bayan shigar shi ofishi, farashin kayayyaki irin garri, shinkafa da wake ya karu yayin da kuma faduwar darajar naira in an kwatanta da dala ya yi kasa.
Matsin tattalin arzuki ya sa iyalai da dama rage abincin da suke ci, yayin da kuma yunwa da rashin isasshen abinci ke karuwa.
Duk da karuwar wahalhalun, Tinubu ya cigaba da kasancewa da kwarin gwiwa, inda ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su hada kai a wurin addu’a da aiki domin cigaban kasar.
“Ina yin fata ta gari ga dukkanin Musulmi da ke azumin watan Ramadan. Ina fatar albarkatun da ke cikin wannan watan mai tsarki su haska zukatanmu da gidajenmu.” Kamar yadda ya karkare da cewa.