Ofishin kula da ayyukan jin kai na majalisar dinkin duniya (OCHA) ya bayyana cewa yawan mutanen da suka bar muhallansu a Sudan sakamakon yaki ya haura miliyan 7,400,000.
“Sama da mutane miliyan 7.4 suka bar muhallansu a ciki da zuwa wajen Sudan tun bayan da yaki ya barke a tsakanin sojojin kasar Sudan (SAF) da kuma dakarun RSF a ranar 15 ga watan Afirilun shekarar 2024.” Ofishin na OCHA ya bayyana kamar yadda ya ke a cikin wani rahoto na kafar watsa labaru ta Vanguard.
Yawan mutanen da suka bar muhallansu a Sudan ya karu da kusan 611,000 a cikin watan da ya gabata, inda da yawa suka bar muhallansu a Gezira da sauran jihohi, kamar yadda OCHA ta bayyana.
“Yaduwar yaki a tsakanin SAF da RSF zuwa tsakiya da gabashin Sudan, wanda nan ne yankin noman hatsi na kasar, ya haifar da hauhawar wahalhalu da bukatar taimako.” Kamar yadda ofishin ya bayyana.
Kamar yadda ofishin na majalisar dinkin duniya ya bayyana, rashin tsaro, sace-sace, gudanarwar gwamnati mai hade da matsaloli, rashin sabis mai kyau da sabis na wayar hannu mara kyau sosai, rashin kudade a hannu da rashin ma’aikata na musamman da na aikin agaji na shafar kai kai kayan agaji.
Ofishin ya kara da cewa bukatar taimako na Sudan da kuma shirin samar da shi kashi 3.1 ne cikin 100 kawai aka samar zuwa ranar Lahadi.
Kasar Sudan dai na fuskantar mummunan rikici a tsakanin Sojojin kasar Sudan (SAF) da kuma dakarun RSF tun ranar 15 ga watan Afirilun 2023, wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane sama da 12,000, kamar yadda kididdigar OCHA ta baya-bayan nan ta bayyana.