Saudi Arabiya ta shirya bude shagon giya na farko, domin amfanin ‘yan diflomasiyya kawai, wanda hakan ya kawo karshen tsatstsauran haramcin giya a masarautar.
Kamar yadda Middle East Eye ta ruwaito, wata majiya ta shaidawa Reuters cewa shagon za a bude shi ne a yankin ‘yan diflomasiyya da ke birnin Riyadh, kuma za a “tsaurara cewa ga wadanda ba musulmai ba ne kawai.”
Ana sa ran bude shagon ne a cikin makonni masu zuwa.
Tun da aka haramta ta a hukumance a shekarar 1952, masarautar ta tsaurara haramta duk wasu kayan shaye-shaye na giya a kasar, ba tare ma da bayyana ban da kalilan ba da wasu kasashen da ba a shan giya makwafta na Gulf kamar Hadaddiyar Daular Larabawa da Katar suka yi.
Yayin da ana shan giya ba tare da an sani ba a kodayaushe a kasar (inda jami’an kasashen waje sukan samu ta hanyar jakar diflomasiyya) sabon shagon na nuni da shagon farko da ke kan doka na sayar da ruwayen giya – wani yunkuri da ake kyautata zaton zai bata ran musulmai masu ra’ayin rikau wadanda ke kallon amfani da giya a matsayin haramtacce a koyarwar musulunci.
Yunkurin ya zo ne bayan dokokin da aka bayyana ta hanyar kafofin sadarwa na cikin kasar da ke da niyyar “dakatar da rashin bin ka’ida wajen musayar” giya a tsakanin gidajen ‘yan diflomasiyya.
Wani jawabi daga gwamnatin Saudiyya a ranar Laraba ya bayyana cewa hukumomi suna kirkiro “sabon tsarin doka … Domin dakatar da safarar kayayyakin giya da abubuwan da aka hada daga gareta wanda ba kan ka’ida ya ke ba daga ma’aikatan diflomasiyya.”
“Sabon tsarin zai mayar da hankali ne wajen samar da kayan giya kayyadajju yayin shiga masarautar domin kawo karshen tsarin na baya da ba ya da ka’ida da ya haifar da rashin ka’ida wajen musayar kayayyaki a masarautar.”
Shekaru da dama na haramci
Yariman Saudiyya Mohammed bin Salman ya dage wajen samar da sauye-sauye a cikin al’unma a masarautar a matsayin wani bangare na “Saudi Vision 2030.”
Ya dakatar da hana mata tuka mota da aka yi a shekarar 2018 ya kyale taron wakoki da kuma yawaitar silima, duk da haka da dira kan masu sassaukan ra’ayi da wadanda ke da ra’ayin rikau a masarautar wadanda ke suka kuma tare da hana bayyana ra’ayi na daban.
Sai dai, duk da jita-jita, akwai rashin amincewa daga jama’ar kasa a kan duk wata shawarar haramtawar ta tsawon shekaru 72.
Haramtawar ta shekarar 1952 ta zo ne bayan wani al’amari da ya faru da ya hada da Yarima Mishari bin Abdulaziz Al Saud da dan diflomasiyyar Birtaniya, Cyril Ousman.
A yayin wani biki wanda dan diflomasiyyar ya halarta, wanda ya ke mataimakin shugaban ofishin Birtaniya a Jeddah, Yariman mai shekaru 19 ya harbe Ousman har lahira bayan ya ki kara masa giya mai yawa.
Biyo bayan kisan – inda aka yankewa Yarima Mishari hukuncin daurin rai-da-rai – Sarki Abdulaziz ibn Saud, wanda ya kirkiro sabuwar kasar Saudiyya, ya haramta duka giya a kasar.
Mutanen da aka samu da laifin shan giya a Saudi Arabiya a da za a iya yi masu hukuncin tara, dauri na wani lokaci, bulala a bainar jama’a da kuma mayarwa kasarsu idan ‘yan kasar waje ne.