Sauya fasalin haraji zai amfani ‘yan Nijeriya ne, ba jefa su cikin uƙuba ba, cewar Ministan Yaɗa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa sauya fasalin raba kuɗin haraji da ake so a yi zai kawo sauƙi da alfanu ne, maimakon sanya wahalhalu.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar 3 ga Disamba, 2024, Idris ya jaddada cewa an yi sauye-sauyen ne domin ƙarfafa wa ‘yan ƙasa gwiwa da kuma bunƙasa cigaba mai ɗorewa.

Ya ce: “Sake fasalin harajin ba zai talauta wata jiha ko wani yankin ƙasar nan ba, kuma ba zai kai ga rufewa ko raunana wata hukumar tarayya ba.”

Ya ƙara da cewa sauye-sauyen za su samar da ƙarin albarkatu ga ƙananan hukumomi, da tabbatar da ingantattun ayyuka da ababen more rayuwa ga ‘yan Nijeriya.

Idris ya kuma yaba da zazzafar muhawarar da ake yi a faɗin ƙasar nan kan ƙudirin sake fasalin harajin, yana mai bayyana hakan a matsayin shaida ga cigaban tsarin dimokiraɗiyyar Nijeriya.

Ya ce: “Abin farin ciki ne sosai ganin ‘yan Nijeriya daga kowane ɓangare na rayuwa sun fito don bayyana ra’ayoyin su kan waɗannan batutuwa masu muhimmanci a ƙasa. Wannan shi ne ainihin jigo da ma’anar dimokiraɗiyya.”

Ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da tattaunawa a mutunce, tare da yin gargaɗi kan yaɗa labaran ƙarya ko amfani da kalaman raba kan jama’a.

Tuni dai Shugaba Tinubu ya umurci Ma’aikatar Shari’a da ta haɗa kai da Majalisar Dokokin Ƙasa don magance duk wata matsala da ta taso game da ƙudirin.

“Gaba ɗaya, waɗannan gyare-gyaren ba kawai za su sauƙaƙe ƙarin kuɗaɗen shiga ba (ba tare da sanya ƙarin nauyin haraji a kan jama’a ba), za su kuma ba da dama ga ‘yan ƙasa su nemi ɗaukar alhaki cikin kula da dukiyar jama’a a dukkan matakan gwamnati,” inji Idris.

A ƙarshe, minisan ya ce gwamnati za ta zuba kuɗaɗen da aka tara ta waɗannan sauye-sauye a muhimman fannoni kamar kiwon lafiya, ilimi, sufuri, da fasaha, ta yadda za a tabbatar da cewa dukkan ‘yan Nijeriya sun ci gajiyar shirin Sabunta Fata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *