Domin nuna hadin kan kasa da ruhin Juyin-juya hali, miliyoyin ‘yan kasar Iran ne daga kowanne bangare na rayuwa suka fito kan tituna a fadin kasar domin gudanar da bukin cika shekaru 46 da samun nasarar Juyin-juya halin Musulunci na shekarar 1979.
Kamar yadda kafar watsa labaru ta Press TV ta ruwaito, bukukuwa da dama da aka gudanar an yi su ne da nuna kishi, wanda hakan ke nuni da zurfin biyayyar mutanen Iran ga akidu da dokokin da suke sune tsarin Jamhuriyar Musulunci ta Iran bayan nasarar Juyin-juya halin.
Daga manyan birane kamar Tehran zuwa kauyuka, ‘yan kasar sun fito domin fareti, dauke da alluna, dauke da tutoci tare da rera wakoki da ke nuni da kyakkyawan al’amari wanda Juyin-juya halin da ya tuntsurar da mulkin Pahlavi ya haifar.
Mutanen, kamar yadda kafar watsa labarun ta bayyana, sun taru ne a wurare sanannu, kamar ‘Azadi Square’ da ‘Enqeleb Square’ da ke babban birnin kasar, inda suke rera taken “Mutuwa ga Amurka” da “Mutuwa ga Isra’ila”, inda hakan ke sake nuni da tsayawar Iran kyam wajen kin shisshigin kasashen waje, nuna fin karfi, da kuma mamaya da tursasawa wadda Yammacin duniya ke goyon baya.
Manyan jami’ai ciki har da shugaba kasa Mosoud Pezeshkian da sanannun manyan sojojin kasar ana sa ran su gabatar da jawabai ga kasar a yayin bukin.
Jawaban ana sa ran za su mayar da hankali kan muhimman abubuwa da dama, ciki har da goyon bayan kasar ga kasashen da ke fuskantar matsi, musamman al’ummar Falasdinawa, Yemen da Lebanon, wanda ke daidai da manufar Juyin-juya halin na rashin goyon bayan mamaya.
Masu sa ido a kan al’amurran yau da kullum sun bayyana cewa nasarar Juyin-juya halin ranar 11 ga watan Fabrairun shekarar 1979 na yin nuni da wani sabon al’amari a tarihin Iran, wanda ya kawar da shekarun fuskantar matsatsi wanda Yammacin duniya ke goyon baya da kafa mulkin da tsarinsa ya ke a cikin tsarin Musulunci tare da goyon bayan jama’ar kasa.