Shirin Amurka na tayar da mutanen Gaza ba zai je ko’ina ba – Khamenei

Ayatollah Ali Khamenei a ranar Talata ya yi watsi da shawarar Amurka na tayar da Falasdinawa daga zirin Gaza wanda yaki ya yiwa illa, inda ya ce “ba zai je ko’ina ba.”

Kamar yadda The New Arab ta ruwaito, Sayyid Khamenei ya bayyana haka ne yayin ganawarsa da shugaban kungiyar Falasdinawa ta Islamic Jihad, Ziyad al-Nakhalah, a Tehran.

“Shirye-shiryen Amurka marasa tsari da wasu shirye-shiryen ta dangane da Gaza da Falasdinu ba za su je ko’ina ba.” A cewar Sayyid Khamenei.

A wannan watan ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi shawarar wani shiri na Amurka ta mallake zirin na Gaza wanda yaki ya yiwa illa kuma al’ummar Falasdinawa da ke yankin su koma wani wurin, ciki har da Misra da Jordan.

Shirin na Trump ya haifar da mayar da martani daga gwamnatocin Larabawa ciki har da Misra da Jordan da kuma daga shugabannin duniya, kuma majalisar dinkin duniya ta yi gargadi kan “kakkabe” Falasdinawa a yankin.

“Ba wani shiri da zai kammala ba tare da amincewar masu fafutika da mutanen Gaza ba.” A cewar Khamenei, inda ya kara da cewa ra’ayin jama’ar duniya yana da goyon bayan Falasdinawa ne.

Tuni dai Iran ta yi watsi da shirin na Trump a kan Gaza, inda ta kira shi da “harin da ba a taba yi ba a baya” a kan dokokin kasa-da-kasa da dokokin da aka sanyawa hannu na majalisar dinkin duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *