Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan sabon Umarnin Zartaswa da ya shafi yadda kuɗaɗen man fetur da gas za su rika shiga asusun gwamnati kai tsaye.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan sabon Umarnin Zartaswa da ya shafi yadda kuɗaɗen man fetur da gas za su rika shiga asusun gwamnati kai tsaye.

Manufar wannan doka ita ce:
👉 a rage satar kuɗi,
👉 tabbatar da gaskiya,
👉 da tabbatar da cewa kowane mataki na gwamnati ya samu haƙƙinsa.

Ga abubuwa 10 da kowa ya kamata ya fahimta:

  1. Kuɗi Kai Tsaye Zuwa Asusun Gwamnati:
    Daga yanzu, kuɗin man fetur da gas ba za su rika bi ta asusu daban-daban ba. Za su shiga Asusun Tarayya kai tsaye, don kada kuɗi su ɓace a hanya, ko a yi habzi da wani kaso.
  2. Jihohi da Kananan Hukumomi Za Su Fi Amfana:
    Za a koma tsarin da Kundin Tsarin Mulki ya tanada, inda Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi za su rika samun rabon kuɗin da ya dace da su.
  3. An Rage Kuɗin da NNPCL ke Riƙewa na Gudanarwa:
    NNPCL ba za ta ƙara ɗaukar kashi 30% ba. Za ta riƙe kashi 20% ne a matsayin kudin gudanarwa daga ribar gas/fetur, sauran kuɗin su tafi asusun tarayya domin raba shi ga matakan gwamnati 3 (Tarayya, Jiha da Ƙaramar Hukuma).
  4. An Soke Asusun Binciken “Frontier”:
    Kuɗin da ake warewa don binciken mai a wasu yankuna an dakatar da su. Yanzu duk kuɗin za su shiga Asusun Tarayya a raba su.
  5. NNPCL Ta Zama Kamfanin Kasuwanci:
    Ba za ta ƙara amfani da matsayinta ta rinjayi farashi ko kashe kuɗi yadda take so ba. Za ta yi aiki kamar sauran kamfanoni na kasuwa.
  6. Kuɗin Tara na Gas Flaring Zai je Asusun Tarayya Kai tsaye:
    Kuɗin tara da ake karɓa idan aka ƙona gas a banza, yanzu za su shiga Asusun Tarayya ne kai tsaye.
  7. ‘Yan Kwangila Za Su Biya Haraji Kai Tsaye (Daga 13 Fabrairu 2026) zuwa ga asusun Tarayya:
    Duk wanda ke aiki a bangaren mai da gas zai rika biyan harajinsa kai tsaye zuwa asusun gwamnati.
  8. Kafa Ƙungiya Ta Musamman Don Kula da Ayyukan Mai:
    An kafa ƙungiya da za ta sa ido kan ayyukan man fetur, domin rage rikice-rikice da saurin warware matsaloli.
  9. An Gyara Rikice-Rikicen da ke cikin Dokoki:
    An daidaita dokokin PIA da tsarin NNPCL don a samu sauƙin aiki da fahimta.
  10. An Daƙile Ɓarnar Kuɗi:
    Ba za a ƙara kashe kuɗi a ayyukan da ba su da amfani ko tasiri ba.

A TAKAICE:
Wannan sabon umarni yana nufin:
✔ kuɗin ƙasa su riƙa zuwa inda ya dace,
✔ Jihohi da Kananan Hukumomi su fi samun kuɗi,
✔ za a rage satar kuɗi da almubazzaranci,
✔ za kuma a ƙarfafa tattalin arzikin Najeriya.

Idan aka aiwatar da shi yadda ya kamata, sauyi ne da kowa zai amfana.

Menene ra’ayinku? Kuna ganin wannan mataki zai inganta tattalin arzikin ƙasa?
Ku yi mana sharhi a ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *